Sai an yi zagaye na biyu: Kwamitin dattijai ya soke zaben da aka yi a kan kyakyawar budurwa, Khadija, a Bauchi

Sai an yi zagaye na biyu: Kwamitin dattijai ya soke zaben da aka yi a kan kyakyawar budurwa, Khadija, a Bauchi

Kwamitin dattijan Giade ya soke nasarar Yunusa a matsayin masoyin Khadija da yayi nasarar lashe zaben auren Khadija.

Hukuncin da aka yanke a ranar Asabar, 15 ga watan Fabrairu, 2020 wajen karfe 10:15 na safe ya soke nasarar Yunusa ne tare da bada umarnin a yi sabon zabe cikin kwanaki bakwai.

Idan zamu tuna, Khadeeja ta fada soyayyar Yunusa da Ibrahim ne wanda hakan yasa aka yi sabon zaben da zai bayyana wanda zai aureta. A karshen zaben kuwa Yunusa ya bayyana a matsayin mai nasara.

Korafin da Kwamitin dattijan Giade suka yanke hukuncin ya biyo bayan korafin da abokin adawar Yunusa ya mika ne. Ibrahim ya zargi cewa zaben da ya bayyana Yunusa mai nasara ya cika da magudi.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya

Ibrahim, wanda ya ce an yi zaben ne a lokacin da mafi yawan magoya bayansa suka tafi aiki saboda da yawansu ma'aikatan gwamnati ne.

Shugaban karamar hukumar Giade, Alhaji Musa, ya soke zaben tare da cewa bai cika sharuddan kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Kundin tsarin mulkin kuwa ya ce kowanne zabe dole a yi shi ranar Asabar, a don haka aka soke wannan.

Ya bada umarnin yin sabon zabe wanda aka amince da yi a ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu 2020 a garin Giade da ke jihar Bauchi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel