Jiragen yakin Najeriya sun yi watsa watsa da sansanin yan Boko Haram a Borno

Jiragen yakin Najeriya sun yi watsa watsa da sansanin yan Boko Haram a Borno

Rundunar Sojan saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa jiragenta sun tarwatsa wata sansanin mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP, wani tsagen tawariyya daga kungiyar Boko Haram, dake jahar Borno.

Daily Trust ta ruwaito rundunar ta bayyana cewa ta kai wannan hari ne a sansanin yan ta’addan ISWAP dake Kirta Wulgo a kan gabar tafkin Chadi dake yankin Arewacin jahar Borno.

KU KARANTA: Yan Fim sun yi tir da shugaban hukumar tace fina fina game da yunkurin kama A Zango

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Daraktan watsa labaru da hulda da jama’a, Air Commodore Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu a babban birnin tarayya Abuja.

Daraktan watsa labaru da hulda da jama’a, Air Commodore Ibikunle Daramola yace Sojojin saman sun kai harin ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Feburairu a karkashin rundunar tsaro ta Operation Lafiya Dole.

Ya kara da cewa harin ya biyo bayan samun kwakkwaran bayani game da wasu sansanoni da yan ta’addan ISWAP suke amfani dasu wajen zaunar da mayakansu tare da horas dasu, sojoji sun gano hakan ne ta hanyar amfani da na’urorin leken asiri tare da tattara bayanai.

“Ba tare da bata lokaci ba sashin Sojan sama na rundunar Operation Lafiya Dole ta aika da jiragen yakin na musamman zuwa sararin samaniyar yankin, inda suka yi luguden wuta a sansanonin, wanda hakan yayi sanadiyyar tarwatsasu duka.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Daramola ya bayyana cewa zasu cigaba da kai hare haren sama tare da aiki da dukkanin jami’an tsaro a yankin Arewa maso gabas wajen karya lagon yan ta’adda tare da kawo karshen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas.

A wani labarin kuma, babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi ma wasu dakarun rundunar Sojan Najeriya dake aiki a karkashin rundunar tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso gabas, Operation Lafiya Dole karin girma zuwa mukami na gaba.

Buratai ya yi ma wadannan Sojoji karin girma ne bisa gagarumar gudunmuwar da suke bayarwa wajen yaki da ta’addanci, ta hanyar jarumtar da suke nunawa a fagen daga yayin arangama da mayakan Boko Haram.

Sojojin sun hada da Warrant Officer Felix Ugwu, wanda aka kara masa girma zuwa Master Warrant Officer, Corporal Kehinde Goban wanda aka kara masa girma zuwa Sergeant, yayin da Private Ishaq Yusif kuma aka kara masa girma zuwa Lance Corporal.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel