Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya

Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya

Babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan yada labarai, Garba Shehu, ya danganta karuwar rashin tsaro a kasar nan da rikicin Libya. Ya ce hakan ne ke sa shigowar makamai kasar nan.

Shehu ya sanar da hakan ne a shirin 'Good Morning Nigeria' a yayin martani ga kiran da 'yan kasar nan suke na sauya shugabannin tsaro, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Shehu ya bayyana cewa, koma bayan da ake samu wajen nasara a kan yaki da Boko Haram na faruwa ne saboda rikicin kasar Libya wanda ke kawo shigowar makamai cikin kasar nan.

Kamar yadda ya ce, rundunar sojin Najeriya na aiki mai kyau kuma kamata yayi 'yan Najeriya su goyi bayansu.

Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya
Fadar shugaban kasa ta bayyana kasar da ta hana Najeriya zama lafiya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sabbin masarautu: Kotu ta yi watsi da karar masu hannu a nada sabon Sarki

Ya ce, "sojojinmu na kokari ba kadan ba, ba zaune suke ba. Amma kuma kalubalen da suke fuskanta ya zama sakamakon wasu lamurra da ke faruwa a yankin. Kamata yayi 'yan Najeriya su nuna godiyarsa tare da tausayawa garesu."

"Sallamar shugabannin tsaron kasar nan ba shine ba. A tunanina Shugaban kasa ba dan koyo bane tun farko. Kwamandan rundunar soji ne, tsohon shugaban kasar mulkin soji ne kuma yana sauraron shawarar ma'abota sani a bangaren tsaro. Bai dace ba a ce mutane na magana a kan abinda basu da kwarewa kuma basu da damar yanke hukunci a kai. Ina fatan banyi magana cike da alfahari ba, amma gaskiya ce nake fadi." ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel