Kaduna-Abuja: A kullum maaikatan Jirgin kasa da Yan sanda na zambar N450,000 zuwa N1m

Kaduna-Abuja: A kullum maaikatan Jirgin kasa da Yan sanda na zambar N450,000 zuwa N1m

Matafiya masu bin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun koka kan zambar tiketin ya zama ruwan dare a tashar jigin Idu (Abuja) da Rigasa (Kaduna).

Matafiyan sunce akwai wasu macuta a tashoshin jirgin wanda suka maida zamba sana’a suna kwaran mutane.

Sun bayyana cewa zambar na kaiwa kimanin N450,000 zuwa N1m a kullum.

Rahotanni sun bayyana cewa matafiyan suna fuskantar kalubale wajen siyan tiketin zuwa Abuja, saboda yanda ma’aikatan jirgin suke boye tiketin sannan su siyar ma wasu wanda zasu siyar akan farashi mai tsada.

Kaduna-Abuja: A kullum maaikatan Jirgin kasa da Yan sanda na zambar N450,000 zuwa N1m
Kaduna-Abuja: A kullum maaikatan Jirgin kasa da Yan sanda na zambar N450,000 zuwa N1m
Asali: UGC

Blue print ta tattaro cewa jim kadan bayan tashin jirgin, ma’aikatan zasu fara siyar da tiketin akan farashinsa ga masu san tsayuwa cikin jirgin, kuma hakan yana jawo chunkoso a jirgin.

Duk da haka,kudin tiketin tsakiyar safe da rana N1,300 da N1,500 na sassafe da yamma,shi wasu ke siyarwa akan N2,000,N 2,500 har N3000 tare da hadin bakin ma’aikatan.

Abin yafi wuce gona da iri ranar lahadi da kuma lokutan hutu,yawanci akan wa’inda suke so su koma aiki da kuma ranar juma,a a tashar jirgin Abuja ga wa’inda suke san zuwa Kaduna.

KU KARANTA Yan ta'addan Boko Haram sun kai jihar Yobe, sun yi barna

Kaduna-Abuja: A kullum maaikatan Jirgin kasa da Yan sanda na zambar N450,000 zuwa N1m
Kaduna-Abuja
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.

Daily Nigerian ta ruwaito lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel