Yan ta'addan Boko Haram sun kai jihar Yobe, sun yi barna

Yan ta'addan Boko Haram sun kai jihar Yobe, sun yi barna

Wasu yan taaddan Boko Haram a ranar Lahadi sun kai hari garin Babangida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeriya.

Kakakin hukumar soji ya bayyanawa manema labarai cewa yan taaddan sun yi kokarin kai farmaki ne birnin jihar, Damaturu amma suka fuskanci wuta daga hannun Sojojin da suka kawar da su.

Har yanzu ba'a bayyana adadin yan ta'adda ko Sojin da suka jikkata ba.

Wani babban jami'in tsaro ya bayyana cewa mazauna garin Babangida sun arce cikin daji yayinda wasu suke boye cikin gidajensu lokacin da aka kai harin.

Jamiin tsaron wanda aka sakaye sunansa ya bayyana cewa yan taaddan sun shiga garin ne da manyan motocin yaki biyar kuma sun ajiye biyu a wajen garin.

Yan ta'addan Boko Haram sun kai jihar Yobe, sun yi barna
Yan ta'addan Boko Haram sun kai jihar Yobe, sun yi barna
Asali: UGC

KU KARANTA Yanzu-yanzu: Kotu ta haramtawa INEC soke jamiyyun siyasa 74

Wani mazaunin garin ya ce yan ta'addan sun kona tsaunin yanar gizon kamfanin sadarwa.

“Wani ya fada min cewa ya ga yaran suna kona tsaunin MTN da Airtel a garin“

Mataimakin kakakin Sakta 2 na rundunar Operation Lafiya Dole, Damaturu, Chinonso Oteh, ya tabbatar da harin.

Ya ce yan taaddan sun yi niyyar shiga birnin Damaturu ne.

Yace “ A hakikanin gaskiya, garin Babangida wadannan yaran ke haduwa kafin sun karaso Damaturu.“

“Basu samu nasarar shiga Damaturu ba ne saboda ruwa wutan da ska sha daga Sojin sama da kasa.“

“Komai ya dawo daidai yanzu. Babu wani abun tsoro.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel