Rundunar Sojan sama ta musanta rahoton kashe mayakan Boko Haram 250

Rundunar Sojan sama ta musanta rahoton kashe mayakan Boko Haram 250

Rundunar Sojan sama ta Najeriya ta bayyana rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai dakarunta sun kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda 250, a matsayin labarun kanzon kurege.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan labari ya fara yawo a kafafen sadarwa ne tun a ranar 13 ga watan Feburairu, kuma wai ya fito ne daga wajen wani mutumi mai suna ‘Comr Aminu Shuaibu Musawa, kamar yadda hukumar sojan sama ta bayyana.

KU KARANTA: Harin yan bindiga: Ministan sufuri Amaechi ya tsallake rijiya da baya a jahar Kaduna

“Hukumar sojan sama tana sanar da jama’a cewa labarin karya ne, kuma duk munanan hotunan da ake watsawa tare da labaran duk karya ne, domin kuwa ba daga rundunar Sojan sama suka fito ba.

“Muna kira ga kafafen watsa labaru da ma sauran jama’a da su sani cewa duk wani ingantaccen rahoto game da aikin rundunar Sojan sama zai fito ne daga bakin daraktan watsa labaru da hulda da jama’a na rundunar.” Inji daraktan watsa labaru da hulda da jama’a, Air Commodore Ibikunle Daramola.

Ibikunke ya cigaba da cewa duk wani sahihin labari daga rundunar za’a sakeshi a yanar gizon hukumar sojan kasa watau www.airforce.mil.ng tare da sauran shafukan rundunar Sojan sama a kafafen sadarwar zamani.

“Duk wani rahoto da ya fito daga wata majiya ta daban ba tare da tantancewa daga rundunar Sojan sama ba, toh jama’a su yi watsi da shi, domin kuwa ba shi da tushe balle makama.” Inji shi.

Daga karshe Ibikune yace tuni rundunar ta fara aikin binciko wadanda ke da hannu cikin kirkirar wannan labari domin gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo a kan tuhumar laifin watsa labaran karya a cikin al’umma.

A wani labarin kuma, fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.

Daily Nigerian ta ruwaito lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel