Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa

Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa

- A kodayaushe dai na Allah basu karewa a cikin al'umma, komai kuwa gurbacewarsu

- Wani dan sanda ne ya dau alwashin yi wa Musulmi da Musulunci hidima da kudin shi

- Hakan ce kuwa ta sa ya fara da gina Masallaci da wajen alwala a matsayin Fisabilillah

A kodayaushe dai na Allah basu karewa a cikin al'umma. Komai kaurin suna da ake fadi a kan wani aiki,, sai ka ga Ubangiji ya saka nagari a ciki.

Duk da aikin addini kuwa ko yi wa addini hidima ba a danganta shi da irin aikin da mutum ke yi.

Wani dan sanda ne ya dau alwashin yi wa Musulmai da Musulunci hidima da albashinsa.

Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa
Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa
Asali: Twitter

Dan sandan ya ce zai kashe dukiyarsa saboda gina Musulunci da Musulmai da izinin Ubangiji. A don haka ne kuwa ya fara da gina masallaci inda daga bisani ya gina wajen alwala.

Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa
Dan sanda ya gina Masallaci da albashinsa
Asali: Twitter

Wannan kuwa ya ci karo da yadda ake kallon 'yan sandan Najeriya, wannan na bayyana cewa ko ina dai ana iya samun nagari. Wannan mutumin ya cancanci jinjina da kuma addu'ar Musulmi baki daya.

Muna fatan Ubangiji ya saka masa da mafificin alkhairi ya kuma karo ire-irensu a cikin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel