Miji ya saki matarsa da ke koya wa kawaye yadda zasu kashe namiji idan ya ci amanarsu

Miji ya saki matarsa da ke koya wa kawaye yadda zasu kashe namiji idan ya ci amanarsu

Wani sabon ango mai suna Chidubem ya saki matarsa mai suna Vivian Chidinma bayan wani tsokaci da tayi a kan yadda mata zasu kashe mazansu masu cin amana a saukake.

A wani tsokaci da Chidubem ya ga matarsa tayi a wani dandali a kafar sadarwa ta Facebook mai suna “Extraordinary mums and singles”, hankalin sabon angon ya matukar tashi.

Matar ta nuna goyon bayanta ga mata masu kashe mazansu da ke cin amanarsu. Ta shawarci matan su dau dabararta a maimakon saka wuka su kashe miji wanda hakan ke jefa su cikin babbar matsala.

"Ina rokon mata da su daina saka wuka suna kashe maza. Idan namiji ya ci amanarki kawai ki je motarsa ne ki cire birki. Tashin hankalin da zai shiga idan ya gano ba birki kuma yana kan titi zai iya halak shi. Idan mai tsawon rai ne zai raunata kashin bayansa ko kuma kafafuwansa biyu su nakasa. daga nan kinga mallakinki ne kadai," ta wallafa.

DUBA WANNAN: Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram

A cewarta, zai fi idan mace ta cire birkin motar mijin wanda hakan zai sa shi mummunan hatsari wanda zai kawo mutuwa ko raunika masu tsanani.

Kamar yadda jaridar Arise News247 ta ruwaito, wata mata a dandalin da ta fusata da tsokacin matar ce taje shafinta na Facebook inda ta ga hotunan bikinta da ba ta dade da wallafa su ba. Hakan ne ya tabbatar da cewa bata dade da yin auren ba.

Miji ya saki matarsa da ke koya wa kawaye yadda zasu kashe miji idan ya ci amanarsu
Miji ya saki matarsa da ke koya wa kawaye yadda zasu kashe miji idan ya ci amanarsu
Asali: Twitter

Daga nan ne fa ta dau tsokacin matar tare da tura wa mijinta.

An gano cewa ta goge tsokacin tare da goge shafinta na Facebook. Daga baya kuwa sai aka gano cewa mijin ya rabu da ita ne don ya ce ba zai amince da yarintarsa ya mutu a hannun wannan muguwar matar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel