Shekau: Babu wanda ya isa ya sa ni in yi tsit Inji Audu Bulama Bukarti

Shekau: Babu wanda ya isa ya sa ni in yi tsit Inji Audu Bulama Bukarti

A wani bidiyon da shugaban ‘Yan ta’addan kungiyar Boko Haram ya fitar kwanan nan, an ji ya na gargadin Bulama Bukarti tare da wasu shugabannin gwamnati da Sojojin Najeriya.

Abubakar Shekau ya kuma ja-kunnen Ministan sadarwan Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami da shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaban hafsun Soji, Janar TY Buratai.

Bulama Bukarti wanda Masanin shari’a ne kuma Mai karatun Digirinsa na uku watau PhD a Jami’ar SOAS ta Ingila, ya fito ya maida martani bayan jawabin Abubakar Shekau.

Audu Bulami Bukarti ya nuna cewa ya san dalilin da ya sa ya zama kayar-bayan ‘Yan kungiyar ta’addan Boko Haram. Audu Bukarti ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita.

A cewar Malam Bulama Bukarti wanda bincikensa daga cibiyar Tony Blair ta Duniya su ka zagaye ko ina, ‘Yan Boko Haram su na kokarin toshe bakinsa ne, wanda ba zai yiwu ba.

KU KARANTA: Boko Haram ta na yi wa Bukarti, Pantami, BBC barazana

Shekau: Babu wanda ya isa ya sa ni in yi tsit Inji Audu Bulama Bukarti
Bukarti ya yi magana game da Shekau a Ranar Juma’a
Asali: Twitter

Duk da wannan barazana, Bulama Bukarti ya bayyana cewa ba za a taba tursasa masa ya yi gum ba, hakan ya na nufin zai cigaba da magana game da ‘Yan ta’addan na Boko Haram.

Ya kamata ya (Shekau) ya ji ni da kyau da babbar murya, Ba za a taba tursasa ni in yi gum ba! Ba za a taba tursasa ni in yi gum ba!! Ba za a taba tursasa ni in yi gum ba!!! Inji sa.

A bidiyon na mintuna 15 da rabi, Shekau ya ce: Bulama Bukarti da ke Ingila, ka ji sakon da na aiko (gare ka). Kai karamin kwaro ne. Iyayen gidanka ma ba za su iya fada da mu ba.

Kwanan nan Audu Bulama Bukarti ya yi wani rubutu inda ya binciko tarihon Boko Haram da hadarin ta’addancinsu. A wannan bincike, Bukarti ya yi magana a kan shi Shekau.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel