Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya sha da kyar a wajen kallo kwallo

Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya sha da kyar a wajen kallo kwallo

A ranar Asabar ne mataimakin gwamnan jihar Kwara ya sha da kyar a wajen rufe gasar wasanni da aka yi ta shekarar nan a jihar Kwara.

Masu kallo da kuma wasu wakilai sun nemi maboya ne bayan da daliban Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zaria suka kai wa jami'an wasan hari, bayan busa husir din karshe na kammala wasan kwallon kafar. Hakan kuwa ya jawo martani mai zafi daga wajen daliban Polytechnic din jihar Kwara.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa anyi wasan karshe ne tsakanin daliban Polytechnic din jihar Kwara da na Nuhu Bamalli da ke Zaria inda aka tashi 1-0.

Amma kuma rikici ya barke bayan da 'yan wasan suka hari lafarin wasan, Adeola Salami. Wannan kuwa yasa daliban jihar Kwara din suka fara jifa da miyagun makamai zuwa cikin filin bayan da aka hana su shiga filin.

A yayin da lamarin yayi kamari, jami'an tsaron da ke wajen sai suka hanzarta yin gaba da mataimakin gwaman.

Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya sha da kyar a wajen kallo kwallo
Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya sha da kyar a wajen kallo kwallo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kyakyawar budurwa daga Yola za ta yi tattaki don haduwa da Sulen Garo

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya gano cewa babban alkalin wasan ya rasa agogonsa da husir dinsa yayin da ake cin zarafinsa amma bai samu rauni ba.

Daliban Nuhu Bamalli din sun fusata da kwallon da abokan wasan nasu suka saka a raga a minti na 68 na wasan, lamarin da ya jawo wannan rigimar bayan busa husir din karshe.

A yayin martani a kan wannan cigaban, Lekan Ogunmodede, daya daga cikin mambobin kwamitin ladaftarwa na wasan da ke wakiltar shugaban polytechnic din Rufus Giwa ta jihar Ondo, ya ce ba za a lamunci wannan tashin hankalin ba.

Ya ce kwamitin zai dau mataki ba tare da an bar wani daga cikin masu laifin ba tare da an ladaftar dashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel