Kyakyawar budurwa daga Yola za ta yi tattaki don haduwa da Sulen Garo
Wata kyakyawar budurwa mai suna Honarabul Ameena Ameenu, ‘yar asalin birni Yola a jihar Adamawa ta bayyana cewa za ta yi tattaki zuwa jihar Kano don yin tozali da Murtala Sulen Garo.
Ameena Ameenu, ta sanar da hakan ne a shafinta na Facebook inda ta ce za ta yi tattakin ne a kafa don saduwa da kwamshinan kananan hukumomin na jihar kano.
Kamar yadda ta wallafa: “Assalamu alaikum, gaskiya ina ganin zan je Kano da kafa don neman Honarabul Murtala Sulen Garo, zan shirya yin tafiyar ne a ranar Laraba InshaaAllah.”
Wannan kuwa shine karo na farko da aka samu mace za ta yi wannan tattakin daga wata jihar zuwa wata domin taya murna ga wani dan siyasa.
![Kyakyawar budurwa daga Yola za ta yi tattaki don haduwa da Sulen Garo Kyakyawar budurwa daga Yola za ta yi tattaki don haduwa da Sulen Garo](https://cdn.legit.ng/images/1120/562db369e679bd54.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
DUBA WANNAN: Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram
Al’amarin yin tattakin dai ya zama ruwan dare a tsakanin matasa. Amma kuma masana a harkar siyasa na ganin irin hakan a abun da bai dace ba.
Ko a makon da ya gabata an samu wani saurayi da yayi tattaki daga Katsina inda ya je yi wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje murna a nasarar da ya samu a shari'ar da suka yi a kotun koli. Wannan saurayin kuwa ya samu tarba hannu bibbiyu daga hannun tawagar gwamnan bayan isarsa jihar Kano.
Ba wannan ba kadai aka yi a makon da ya gabata, wani saurayi yayi tattaki don zuwa yi wa Abba Gida-gida da Kwankwaso jajen shari'ar da aka yi a kotun kolin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng