Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutane 33 a Katsina

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutane 33 a Katsina

Akalla mutane 33 sun rasa rayukansu yayinda yan bindiga suka kai mumunan hari kauyukan Tsauwa da Dankari a jihar Katsina.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun kaiwa mutanen harin kwantan bauna inda gaba daua suka rasa yadda zasuyi.

Harin ya auku ne da yammacin Jumaa a karamar hukumar Batsari. Kwamishanan yan sandan jihar Katsina, Sanusi Buba, wanda ya ziyarci wajen ya bayyanawa manema labarai abinda ya faru.

Ya ce yawancin wadanda yan bindigan suka kashe tsaffin mata ne da yara da suka kasa guduwa yayinda sauran jamaa suka arce.

Buba ya ce daga cikin mutane 21 da aka kashe a garin Tsauwa, bankawa 13 wuta akayi har lahira. Hakazalika mutane 9 suka hallaka a garin Dankar.

Masu idanuwan shaida sun bayyana manema labarai ranar Asabar cewa yan bindgian sun dira cikin garin ne kan babura da bindigogi yayinda mutane suka shiga sallar Magariba.

Karamar hukumar Batsari na daya daga cikin kananan hukumomi takwas a jihar Kastina da yan bindiga suka addaba a shekarun kusa.

Duk da matakan sulhu da gwamna jihar, Aminu Masari, ya dauka, har yanzu baa daina garkuwa da mutane da kashe-kashe ba.

Kalli hotunan wuraren da aka kai harin:

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutane 33 a Katsina
Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutane 33 a Katsina
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng