Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram

Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram

A ranar Asabar ne fadar shugaban kasa ta ce 'yan siyasa da masu cin moriyar ta'addancin 'yan Boko Haram na shirya kungiyar mata da maza har dubu biyu don yin zanga-zanga da bukatar a sauya shugabannin tsaron kasar nan a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Babban mai bada shawara ga shugaban kasa a kan fannin yada labarai, Garba Shehu, ya ce fadar shugaban kasar ta samu rahoton da ke bayyana wannan manufar tasu. Ya kara da cewa an yi hayar jama'a ne wadanda suka yi wa Shugaban kasar ihu a ziyarar da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram
Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari

Shehu ya ce, "Wasu 'yan siyasa da masu cin gajiyar Boko Haram a halin yanzu na shirya makarkashiya. Suna biyan jama'a kudi don shirya zanga-zanga. A kalla sun yi hayar mata da maza dubu biyu don yin zanga-zanga a kan sauya shugabannin tsaron kasar nan a ranar Litinin."

"Jam'iyyar PDP na kai da kawowa daga ofishin jakadancin wannan kasa zuwa na waccan kasar don zanga-zanga ga mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma kotun koli. Suna son nuna cewa 'yan Najeriya na goyon bayan abinda suke yadawa a tituna," ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel