Dangin amarya sun lakada wa ango duka a wurin liyafar biki
An yi wa wani ango duka a wajen bikinsa bayan matarsa ta farko ta sanar da amaryar cewa yana da mata biyu. A take kuwa ango Asif Rafiq Siddiqi ya sha duka da mari daga wajen mahalarta bikin. Dangin amaryarsa sun yaga masa kaya kafin ya tsere don ceton kan shi.
A kasar Pakistan an halatta auren mata hudu. Amma duk da haka dole mijin ya shaida wa sauran matan kafin auren.

Asali: Twitter
Siddiqi kuwa bai bi wannan tsarin ba, hakan ne yasa bayan amaryarsa ta samu labari ita da ‘yan uwanta suka lakada masa mugun duka.
Wannan lamarin dai ya faru ne a birnin Karachi. Matar ango ta fari mai suna Madiha Siddiqi ta je wajen bikin ne tare da dansa. Bayan isarta wajen sai ta shaidawa ‘yan biki cewa mijinta ne kuma shine mahaifin yaron. “Ya shaida min zai je Hyderabad ne yayi kwana uku sai jin labarin biki nayi,”

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Shekau yayi martani a kan zuwan Buhari Borno, yayi barazanar kai masa hari
Daga nan ne dangin amarya suka kai amaryar wani daki ta huta sannan suka nemi dalla-dallan labari daga bakin matar.
Madiha Siddiqi ta ci gaba da basu labarin yadda komai ya faru. Ta auresa ne a 2016 lokacin tana karatu a jami’a a Urdu da ke Karachi.

Asali: Twitter
Ta ce, “Bayan munyi aure sai ya je ya sake aure ba tare da ya sanar dani ba a 2018. Bayan na gane hakan sai ya musanta amma daga baya sai ya amince da cewa ya auro mata ta biyu. Matarsa ta biyu ce ta shaida min cewa zai kara aure na uku inda ta sanar dani wajen aure.”
Nan take kuwa ‘yan uwan amarya suka fusata tare da fara dukansa har da yaga masa kaya.
Jami’an ‘yan sanda ne suka cece angon inda suka hazarta barin wajen da shi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng