Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa tirelolin Dangote 2 wuta bayan sun murkushe mutane 6 har lahira

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa tirelolin Dangote 2 wuta bayan sun murkushe mutane 6 har lahira

Tirelolin Dangote biyu dauke da Siminta sun haddasa hadari wanda yayi sanadiyar rasa rayukan mutane shida a jihar Ogun ranar Asabar, 15 ga watan Febrairu, 2020.

Hadarin ya faru ne misalin karfe 12:20 na rana a old Tollgate, Ota, hanyar Legas zuwa Abekuta a karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar Ogun.

Hakan na faruwa wasu fusatattun matasan da suka shaida hadarin suka bankawa tirelolin wuta.

Sakta kwamanda da hukumar kiyaye hadura kan hanya FRSC, Clement Oladele, ya tabbatar da faruwar hadarin.

Oladele ya yi bayanin cewa hadarin ya shafi motoci da dama kuma ana cikin kwashe wadanda abin ya shafa.

Ya ce hadarin ya auku ne tsakanin motocin Dangote biyu dauke da buhuhunan Siminta, mota kirar Space Wagon da bas kirar Volkswagen.

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa tirelolin Dangote 2 wuta bayan sun murkushe mutane 6 har lahira
Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa tirelolin Dangote 2 wuta bayan sun murkushe mutane 6 har lahira
Asali: Facebook

KU KARANTA Zamu bada N36m ga duk wanda ya gano magani Coronavirus - Gwamnatin tarayya

A cewarsa, matasan sun bankawa motocin dangoten wuta ne saboda su suka haddasa hadarin.

Yace, “`FRSC na wajen kuma an tuntubi hukumar kwana-kwana domin kashe wutar saboda hakan zai saukaka ceton wadanda ya shafa.“

Ya kara da cewa unguwar da hadarin ya faru ya shahara da hadura a hanyar.

Ya ce a shekaru biyar da suka gabata, hanyar ta lashe rayuka 40. Saboda haka, ya yi kira ga direbobi suyi hankali wajen bin hanyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel