Yanzu-yanzu: Wani mutum ya fada tekun jihar Legas

Yanzu-yanzu: Wani mutum ya fada tekun jihar Legas

- Yawan masu kashe kansu a Najeriya na karu a shekaru biyu da suka gabata

- Rahotannin na mutane na fadawa cikin tekun jihar Legas sun ci gaba da yawaita

- Masu ceto a halin yanzu suna ta neman wani mutum da aka gano cewa ya fada cikin tekun jihar Legas a yau Asabar, 15 ga watan Fabrairu

Yawan masu kashe kai a Najeriya ya ci gaba da karuwa tun daga shekarar da ta gabata. An gano cewa yawan jama’ar da ke fadawa cikin tekun jihar Legas na ci gaba da karuwa a kodayaushe

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a yau din nan, wani mutum da ba a gano sunanshi ba ya fada cikin babbar tekun jihar Legas daga gada ta uku.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, a halin yanzu masu ceton sun isa wajen tare da kokarin ceto rayuwar shi.

Har a halin yanzu dai ba a gano mutumin ba kuma ana ta jiran sauran bayanai daga masu ceton.

Kamar yadda wani a kafar sada zumuntar zamani ya wallafa: “Yakamata a haramta hawa babbar gada ta uku. Ina fatan masu ceton su samo shi daga karshe.”

Yanzu-yanzu: Wani mutum ya fada tekun jihar Legas
Yanzu-yanzu: Wani mutum ya fada tekun jihar Legas
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

A shekarar da ta gabata ne cibiyar taimakon gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) suka ceto wani mutum mai matsakaicin shekaru a ranar 15 ga watan Oktoba.

An gano cewa mutumin mai suna Desmond Abraham, ya so kashe kanshi ne don ya fada tekun ne ta babbar gada ta uku. Abraham mai shekaru 44 bai mutu bane sakamakon ceto shi da jami’an hukumar LASEMA suka yi.

An gano cewa Abraham ya so kashe kanshi ne sakamakon matsin rayuwa da kuma tsananin rashin kwanciyar hankali daga iyalan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel