An yi zabe a Bauchi don raba gardama tsakanin samari 2 da ke neman auren wata budurwa (Hotuna)

An yi zabe a Bauchi don raba gardama tsakanin samari 2 da ke neman auren wata budurwa (Hotuna)

An gudanar da wata 'yar kwarya-kwaryar zabe a jihar Bauchi domin a raba gardama tsakanin wasu samari biyu da ke neman auren wata budurwa guda bayan budurwar ta kamu da son samarin biyu da kuma gaza zaban daya daga cikinsu.

A cewar wani mai amfani da shafin Twitter @Mubarack_Umar, budurwar mai suna Khadija ta kamu da son mazan biyu, Inusa da Ibrahim a garin Giade da ke jihar Bauchi.

Bayan da gaza tsayar da guda cikinsu da za ta aura, manyan gari suka yanke shawarar yin zabe domin wanda ya lashe zaben ya zama angon budurwar.

Mutane sun fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'unsu inda daga karshe Inusa ne ya yi nasara da kuri'u mafi rinjaye kuma an mika masa takardan shaidan cin nasarar zabe.

DUBA WANNAN: Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

Ya rubuta cewa, "Khadija ta kamu da son maza biyu ta kuma gaza tsayar da guda a cikinsu; samarin biyu kuma sun ki amincewa daya ya hakura ya bar wa daya.

"Manyan garin Giade a jihar Bauchi (da izinin Khadija) sun gudanar da zabe inda Inusa ya samu kuri'u mafi rinjaye inda ya doke abokin karawarsa Ibrahim."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel