Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya

- Tsohon Golan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Idah Perterside ya bayyana yadda son kudin shi ya kais hi kungiyar asiri

- Ya ce sirrin daukakar shi kuwa shine kwanciya da ‘yan mata ballanta budurwai da kuma shigar dasu cikin kungiyar

- Tsohon Golan ya kara da fadin cewa abin ya kai ya kawo har yana taro da macizai wanda hakan har kusan hauka ya sa shi

Tsohon Golan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, Idah Peterside ya bada labarin yadda mugun son kudin shi ya kai shi ga fada wa kungiyar asiri.

A wata tattaunawa da tsohon Golan yayi da Brila FM a ranar Talata tare da Ifeanyi Udeze, ya ce fadawar shi kungiyar asiri yayi ne ba tare da sanin mutane ba. Ya kara da cewa, sirrin asirin shi shine kwanciya da ‘yan mata budurwa.

Peterside ya ce: “Abin bakin cikin shine yadda na fada bautar shaidan. Na shiga kungiyar asiri ba tare da sanin mutane ba.

Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya
Sirrin dukiya da daukakata ya dogara ne da yawan 'yan matan da nayi lalata dasu - Tsohon golan Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Babbar magana: Na yadda akwai Allah, amma zancen wuta da aljannah kanzon kurege ne a wajena - Efia Odo

“Nayi hakan ne don ina bukatar kudi da suna wadanda duk sai da na same su. Abu yayi Kamari har ina taro da macizai. Gaskiya nawa yayi yawa, abin kamar hauka nayi.

“Abinda ya kaini kololuwar kungiyar ya dogara ne da yawan matan da na kwanta dasu. Dama kuma rantsuwata shine in kai mata. Bana kwanciya da su don soyayya ko dangantaka, kawai burina shine in kai su kungiyar sannan in ci gaba da harkokina.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel