Kamfanin NNPC ta kammala aikin daukan mutane 1050 aiki

Kamfanin NNPC ta kammala aikin daukan mutane 1050 aiki

Hukumar man fetir ta Najeriya, NNPC ta sanar da kammala aikin daukan sabbin ma’aikata aiki da yawansu ya kai mutum 1,050, wanda hakan ya kawo karshen aikin da ta dauka daga shekarar 2019/2020.

Daily Trust ta ruwaito babban manajan hulda da jama’a na kamfanin, Samson Makoji ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, inda ya ruwaito shugaban NNPC, Malam Mele Kyari yana cewa sashin kula da ma’aikata na hukuma ta fara bayar da shaidar daukan aiki ga matasa 1,050 da ta dauka aiki.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya ware naira biliyan 4.7 don baiwa daliban Kaduna tallafi

Kamfanin NNPC ta kammala aikin daukan mutane 1050 aiki
Kamfanin NNPC ta kammala aikin daukan mutane 1050 aiki
Asali: UGC

Da yake bayyana daukan aikin a matsayin wani lamari da aka samu gagarumar nasara, Malam Kyari ya bayyana cewa sakamakon daukan aikin ya nuna hukumar ta dauko sabbin ma’aikatan ne daga sassa daban daban na kasar, tare da cika dukkanin ka’idojin da suka kamata.

Sai dai Malam Kyari yace hukumar za ta cigaba da daukan aiki, musamman bangaren daukan kwararru, wanda yace nan zasu mayar da hankalinsu nan bada jimawa ba.

“Muna tsumayin karbar sabbin ma’aikatanmu domin yin aiki tare dasu don gina kamfanin NNPC wanda duk wani dan Najeriya zai yi alfahari da shi.” Inji shi.

Idan za’a tuna a ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2019 ne NNPC ta sanar da neman daukan ma’aikata, inda a ranar 27 ga watan Maris aka fara karbar takardun masu neman gurbin aiki a hukumar.

A ranar 1 ga watan Yuni kuma aka gayyaci wadanda suka nemi gurbin aiki domin zana jarabawa, yayin da a watan Yuli aka gayyacesu domin amsa tambayoyin baki da baki, daga nan kuma aka ware mutane 1,050 da suka cancanta.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kaduna ta ware kimanin naira biliyan 4.7 domin daukan nauyin daliban jahar Kaduna dake karatu a kasashen waje tare da baiwa wadanda suke karatu a gida tallafi, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana.

Shugaban hukumar Hassan Rilwan ne ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labaru a ranar Alhamis, 13 ga watan Feburairu, a garin Kaduna.

Malam Hassan ya bayyana cewa sun biya kudin tallafi ga dalibai 4,400 a cikin dalibai 7, 598, sa’annan ya kara da cewa sun tura dalibai karatu zuwa kasar Amurka, Birtaniya, Australia, Jamus da kuma Cuba.

“Daga cikin daliban akwai Abba Dauda Maitala wanda ya samu tallafin naira miliyan 15 don yin karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar tsaro na yanar gizo a jami’ar Northumbria dake garin Newcastle, Birtaniya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel