Yanzu-yanzu: Mutum 5 sun mutu wurin hakar ma'adinai a Kano (sunaye)

Yanzu-yanzu: Mutum 5 sun mutu wurin hakar ma'adinai a Kano (sunaye)

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyar cikin shida da kasa ya ruftawa a Ramin Farar Kasa a kauyen Dauni a karamar hukumar Minjibir na jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a a Kano.

Ya ce, "Wani Malam Danlami Murtala kira mu da rana a ranar Alhamis mislain karfe 2.45 na rana daga kauyen Dauni inda ya ce kasa ya ruftawa wasu mutane shida da ke hakar kasa.

"Mun aike da jami'an mu nan take bayan an sanar da mu domin su yi kokarin ceto wadanda abin ya shafa amma wani karamin yaro mai shekaru hudu ne kawai aka samu da rai."

Kano: Mutum 5 sun mutu wurin hakar ma'adinai, wasu 6 sun makale
Kano: Mutum 5 sun mutu wurin hakar ma'adinai, wasu 6 sun makale
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno

Ya bayar da sunan wadanda suka mutu kama haka; Ibrahim Shu’aibu, dan shekara hudu; Dije Shu’aibu, dan shekara 8; Hadiza Shu’aibu, 'yar shekara 12; Nana Idris, 'yar shekara 12; Wasila Nuhu, yar shekara 13; and Sa’ida Lawwali, yar shekara 32.

Muhammad ya ce an mika wa dagajin kauyen, Alhaji Bello Rabi'u gawarwakin wadanda suka rasu inda ya kara da cewa wanda ya yi rai ya samu karaya.

Ya shawarci wadanda ke sana'ar hakar kasa ko kuma ma'adinai su rika kulawa sosai wurin yin ayyukansu domin kiyaye lafiyarsu da rayyukansu kamar yadda kamfanin dillancin labarai, NAN, ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel