Rundunar tsaron yankin Yarbawa Amotekun ta samun amincewar Yansanda

Rundunar tsaron yankin Yarbawa Amotekun ta samun amincewar Yansanda

Babban sufetan Yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya amince da tsarin rundunar tsaro ta yankin Yarbawa, watau Amotekun, bayan gwamnonin jahohin yankin sun rattafa hannu kan tsare tsaren aikin rundunar.

Punch ta ruwaito gwamnonin sun bayyana ma IG Adamu cewa rundunar Amotekun za ta taimaka wajen kare yankin daga ayyukan miyagun mutane, tare da tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu.

KU KARANTA: Buhari ya yi alkawarin sake gina gidajen da Boko Haram ta kona a Auno tare da biyan fansa

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN ne ya bayyana haka a madadin gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya, a yayin taron tsaro na yan doka da babban sufetan Yansandan ya kira a ranar Alhamis a jahar Legas.

A karshen ganawar, babban sufetan Yansanda tare da wakili guda daya daga kowacce jahar kudu maso yamma sun bayyana ma manema labaru amincewarsu da tsarin aikin rundunar tsaro ta Amotekun.

Sai dai babban sufeta Muhammad Adamu yace Amotekun ba zai kasance a karkashin ikon shuwagabannin yankin Yarbawa kamar yadda suka tsara shi da farko ba, inda yace zai kasance a karkashin ikon gwamnati ne.

Don haka yace Amotekun za ta zamo tsarin tsaro ne na yan doka, wanda zasu dinga sa ido a cikin unguwanninsu domin taimaka ma jami’an Yansanda wajen gudanar da aikinsu.

A nasa jawabin, Gwamnan Ondo yace: “Gwamnonin kudu maso yammaci tare da babban sufetan Yansanda sun tattauna game da muhimmancin tsarin tsaro na yan doka wanda zai gudana a karkashin sa idon Yansanda, kuma muma mun amince da tsarin tsaro na yan doka.”

Daga karshe Adamu yace rundunar Yansanda za ta kasance tana da hannu cikin daukan yan dokan Amotekun, horas dasu da kuma turasu wuraren da zasu gudanar da aikinsu.

Zuwa yanzu dai majalisun dokokin jahohin yankin Yarbawa suna ta gudanar da karatuttuka a kan kudurin dokar Amotekun domin bashi madogara a shari’a, majalisun dokokin jahohin Osun, Ogun da Oyo sun bayyana burinsu na tabbatar da kudurin dokar cikin gaggawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel