Kungiyar Musulunci ta yi Allah wadai da ka'idojin daukan ma'aikatan Amotekun
Kungiyar Musulmai mai suna Muslim Association of Nigeria (MAN) ta fusata da yadda aka bukaci shaidar haihuwa daga coci a matsayin ka’idar samun aikin tsaro na Amotekun, kamar yadda jaridar Laila News ta bayyana.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a takardar da shugabanta Alhaji J. O Ojikutu da jami’ar hulda da jama’arta, Alhaja Nurat Adebayo suka sa hannu tare da fitarwa a taron shugannin kungiyar da suka yi kwanan nan.
Kungiyar ta bayyana cewa tana bayan wannan salon tsaron da aka kirkiro da shi a yankin Kudu maso yamma, amma kuma yadda aka sanya addini a sahun gaba ne abin Allah wadai.
Sauran ka’idojin daukar aikin sun hada da shaidar haihuwa daga coci, karamar hukuma ko kuma asibiti, shaidar ko kuma takardar yabo daga inda mutum ya fito.
DUBA WANNAN: Kwace kujerar APC a Bayelsa: Atiku ya yi martani
Kamar yadda takardar ta sanar, “MAN ba ta gamsu da yadda Amotekun ta saka addini a sahun gaba ba wajen daukar ma’aikatanta. Wannan lamarin kuwa ya jawo mata kushe daga jama’a da yawa da ke yankin Kudu maso Yamman.”
Ta kara da cewa, “Kungiyar ta sakankance cewa bai kamata a saka addini ba a yayin da ake zancen tsaro. Gwamnatin Najeriya ta dau alhakin shaidar haihuwa da ta mutuwa tun a 1990. Amma kuma har ila yau, kungiyar tana jinjinawa a kan yadda ake kokarin shawo kan matsalar tsaro a Najeriya ballantana hobbasan da gwamnonin Kudu maso yamman suka yi wajen kirkiro da Amotekun.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng