Da duminsa: Yan majalisar wakilai biyu sun koma APC

Da duminsa: Yan majalisar wakilai biyu sun koma APC

Yan majalisar wakilan tarayya biyu na jam'iyyar Action Alliance (AA) sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a ranar Alhamis, 13 ga watan Febrairu, 2020.

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya sanar da cewa Kingsley Uju da Pascal Obi matsayin sabbin mambobin jam'iyya mai rinjaye.

Kingsley Uju na wakiltan mazabar Ohaji/Egbema/Oguta/Oru West Ideato yayinda Pascal Obi ke wakiltan Ideato. Dukkansu yan jihar Imo.

A wasikar da kakaki Femi Gbajabiamila ya karanta, ya ce yan majalisan sun fita daga jam'iyyar AA ne saboda sabani da rashin sulh tsakaninsu.

A yanzu, cikin yan majalisar wakilai daga jihar Imo 10, APC sun zama hudu yayinda PDP ke da shida.

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, da Rochas Okorocha, sun halarci zaman sauya shekan.

Wannan sauya shekan ya biyo bayan hukuncin kotun koli da ta sallami Emeka Ihedioha na PDP matsayin gwamnan jihar Imo kuma ta maye gurbinshi da Hope Uzodinma na jam'iyyar APC.

Da duminsa: Yan majalisar wakilai biyu sun koma APC
Da duminsa: Yan majalisar wakilai biyu sun koma APC
Asali: Depositphotos

Kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Chiji Collins a ranar Asbar ya bayyana cewa yan majalisar dokokin jihar 26 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Daga cikin yan majalisan dokokin jihar 27, tsohon mataimakin kakakin, Okey Onyekanma, ne kadai ya rage a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), The Nation ta ruwaito.

Yayinda yake jawabi ga mabiya APC a taron nuna goyon baya ga gwamnan jihar, Hope Uzodinma, a Owerri, Chiji Collinsa ya ce yan majalisan shirye suke da baiwa gwamnan goyon baya domin nasara.

Ya jaddada cewa babu wanda ya biyasu kudi domin su sauya sheka.

Yace: "Zuwa daren jiya, yan majalisa 26 sun koma APC, kuma ina tabbatar muku a mako mai zuwa, dukkan 27 zasu zama APC. Ku jira zaman majalisa na gaba inda sukkansu zasu sanar da sauya shekansu."

"Shirye muke da goyawa gwamnan baya saboda ya shirya kawo sauyi jihar."

Kotun kolin ta alanta Hope Uzodinma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) matsayin zakaran zaben gwamnan 9 ga Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel