Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

Ya yi karar matarsa a kotu domin ta hana shi kusantar har tsawon kwanaki 48

Wani dan kasuwa, Ibrahim Lawal, dan shekaru 58 ya yi karar matarsa, Saratu Musa a gaban alkalin kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa a jihar Kaduna saboda ta hana shi hakkinsa na kwanciyar aure na tsawon kwanaki 48.

Ibrahim Lawal da ke zaune a unguwar Maraban Jos a Kaduna ya ce matarsa ta hana shi hakinsa na kwanciyar aure na tsawon kwanaki 48 kuma ya roki kotun shiga tsakani.

Ya ce, "Na yi iya kokari na domin in faranta mata rai har wa'azi ma na yi mata a hakan hadarin da ke tattare da hana ni hakki na na kwanciyar aure amma abin ya ci tura."

Mai gida ya yi karar matarsa a kotu domin ba ta bashi hadin kai wurin kwanciya
Mai gida ya yi karar matarsa a kotu domin ba ta bashi hadin kai wurin kwanciya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ka aureni ko in rasa raina - Budurwa ta fadi warwas a titi (Bidiyo)

A bangarenta, wanda aka yi karar da ke zaune a gida mai adreshi daya da na wanda ya yi karar, ta ce ta hana shi hakkinsa na kwanciyar aure ne saboda ya ki biyan ta bashin Naira dubu 20 da ya karba.

Ta roki alkalin kotun ya tursasa wa mijin ta ya biya ta bashin da ya karba.

Alkalin kotun, Dahiru Bamalli, bayan ya kamalla sauraron bangarorin biyu ya umurci wanda ya yi karar ya biya matarsa bashin da ya karba sannan ya bukaci matar da rika bawa mijinta hakkinsa na kwanciyar aure.

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 6 ga watan Mayun 2020 kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164