Yadda za mu aiwatar da hukuncin kotun koli a kan zaben Bayelsa - INEC

Yadda za mu aiwatar da hukuncin kotun koli a kan zaben Bayelsa - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce za ta yi biyaya ga hukuncin da kotun koli ta yanke a yau na soke nasarar 'yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress’ (APC) a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.

Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban sashin wayar da masu zabe (IVEC), Festus Okoye ya shaidawa Daily Trust yau a Abuja cewa hukumar za ta tallafawa sashin ta na ayyuka domin ta aiwatar da umurnin babban kotun kasar.

"Kotun kolin ta umurci hukumar zaben ta bawa jam'iyyar da ta zo na biyu wurin samun kuri'u shaidar lashe zabe a jihar ta Bayelsa.

Yadda za mu aiwatar da hukuncin kotun koli a kan zaben Bayelsa - INEC
Yadda za mu aiwatar da hukuncin kotun koli a kan zaben Bayelsa - INEC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

"Yanzu abinda hukumar za ta yi shine za ta koma sashin ayyukanta domin gano jam'iyyar da ta zo na biyu a zaben da kuma jam'iyyar da ta samu kuri'u a dukkan yankunan jihar.

"A kan wannan tsarin ne za mu aiwatar da hukuncin na kotun kolin. Za mu aiwatar da hakan da zarar an aiko mana da hukuncin kotun kolin, saboda mu san ainihin abinda kotun kolin ke so mu aikata," in ji Okoye.

A yau Alhamis ne kotun koli ta kwace kujerar zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon da kuma abokin tafiyarsa, Biobarakuma Degi-Eremienyo, wadanda suke ta shirye-shiryen karbar rantsuwar darewa kan karagar mulkin jihar.

Alkalai biyar na kotun, wadanda Mai Shari'a Mary Peter-Odili ta jagoranta, sun umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta janye shahadar haye wa kujerar jagorancin jihar da ta mikawa 'yan takarar jam'iyyar APC din a jihar.

Kotun kolin ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta da ta mika shaidar cin zabe ga jam'iyya mai biye da ta APC din a yawan kuri'u a jihar idan aka duba sakamakon zaben da aka yi a ranar a 2019.

A soke zaben Lyon ne saboda abokin takararsa ya gabatarwa hukumar zabe takardun shaida na bogi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel