An kona wani mutum kurmus saboda ya saci kaza

An kona wani mutum kurmus saboda ya saci kaza

Fusattatun matasa sun kone wani mutum mai suna Victor a Calabar babban birnin Cross Rivers da ake ce ya saci kaza.

A cewar rahoton da Vanguard ta ruwaito, lamarin ya faru ne a ranar Talata misalin karfe 5 na asuba a Abitu Avenue kusa Ekpo Edem da ke kallon cocin Living Faith a Ekpo Edem a karamar hukumar Calabar da Kudu.

Wadanda abin ya faru a gabansu sun ruwaito cewa 'yan banga da masu gadi sun sha kama marigayin amma a kan sake shi da fatan cewa zai dena satar.

A cewar wani ganau da ya nemi a boye sunansa, he ya ce Victor ya zo kaman yadda ya saba domin aikata mummunan abinda ya saba da asubahin amma wannan karon kaza ya zo sata.

An kona wani mutum kurmus saboda ya saci kaza
An kona wani mutum kurmus saboda ya saci kaza
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Ya kara da cewa kukan kazan ne ya saka makwabta suka farka daga bisani kuma mutane su ka yi farautarsa misalin karfe 4 na asuba suka masa dan banzan duka kana suka banka masa wuta.

Da ta ke tsokaci a kan lamarin, mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP Irene Ugbo ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta koka kan yadda mazauna unguwar suka dauki doka a hannunsu. Ta kuma yi alkawarin cewa za su kawar da bata gari a Calabar.

Ta ce, "Ba mu goyon bayan masu laifi ko abinda su ke aikatawa amma ya zama dole mutane su gane cewa daukan doka a hannu laifi ne, kamata ya yi su mika wadanda ake zargin hannun 'yan sanda domin ayi bincike kuma a gurfanar da su a kotu."

Ta kara da cewa duk wanda aka samu yana daukan doka a hannunsa zai fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel