Yanzu Yanzu: Gobara ta kama a kasuwar Mile 12 da ke Lagas

Yanzu Yanzu: Gobara ta kama a kasuwar Mile 12 da ke Lagas

- Gobara ta kama shahararriyar kasuwar nan ta Mile 12 da ke jahar Lagas

- Koda dai babu cikakken bayani kan lamarin a daidai kawo wannan ta, wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sadarwa sun nuna yadda kasuwar ke ci da wuta bal-bal

- Lamarin ya afku ne a safiyar yau Alhamis, 13 ga watan Fabrairu

Rahotanni da ke zuwa mana daga New Telegraph ya nuna cewa shahararriyar kasuwar nan ta Mile 12 da ke jahar Lagas na nan tana ci da wuta.

Koda dai babu cikakken bayani kan lamarin a daidai kawo wannan ta, wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sadarwa sun nuna yadda kasuwar ke ci da wuta bal-bal.

An tattaro cewa gobarar ta fara ne da sassafiyar ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu.

Legit.ng ta lura cewa a yan kwanakin nan kasuwannin kasar na ta Kama wa da gobara, lamarin da ya sanya yan Najeriya da dama cikin fargaba.

A wani labarin kuma, mun ji cewa an shiga cikin tashin hankali da dimuwa yayin da wata mummunan gobara ta tashi a gidan tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo dake garin Abekuta, babban birnin jahar Ogun.

Jaridar The Nation ta ruwaito gobarar ta tashi ne a daren Laraba, 12 ga watan Feburairu, da misalin karfe 9:30 a gidan dake unguwar Ita-Eko dake cikin garin Abekuta, sai dai shaidun gani da ido sun bayyana cewa lantarki ne ya janyo gobarar.

KU KARANTA: Neman a sauya salon tsaron kasar: Kungiyar gwamnoni ta yaba ma Zulum

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da kyar da sudin goshi makwabta da ma’aikatan gidan suka samu nasarar kashe wutar bayan sun mata taron dangi bayan sun kwashe kimanin awa daya suna fama da ita.

Shaidun sun bayyana cewa wutar ta yi ta tashi daga wani sashi zuwa wani sashin gidan saboda iskar bazara.

Sai dai daraktan hukumar kashe gobara na jahar Ogun, Fatai Adefala ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma yace wutar ta cinye iyakar wani dakin ajiyan kaya ne, ba wai asalin gidan ba. Sa’annan yace jami’an hukumarsu sun kashe wutar da kayan aikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel