Kaduna: 'Yan bindiga sun budewa 'yan kasuwa wuta, sun kashe 7

Kaduna: 'Yan bindiga sun budewa 'yan kasuwa wuta, sun kashe 7

Wasu mutane wadanda ake zargin 'yan bindiga ne sun budewa wasu 'yan kasuwa wuta da daren Laraba a kasuwar Maro da ke masarautar Kajuru ta jihar Kaduna. 'Yan bindigar sun halaka mutane bakwai a kasuwar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa lamarin ya faru ne wajen karfe 7 na yamma, yayinda 'yan kasuwar ke kokarin tashi.

Wata majiya mai kusanci da dagacin Kufana din ta tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis. Majiyar ta ce maharan sun budewa 'yan kasuwar wuta ne inda suka kashe bakwai daga ciki amma sun raunata mutane ba adadi.

Ya ce maharan sun isa kasuwar ne a ababen hawansu sannan suka fara harbi ta ko ina.

Kaduna: 'Yan bindiga sun budewa 'yan kasuwa wuta, sun kashe 7
Kaduna: 'Yan bindiga sun budewa 'yan kasuwa wuta, sun kashe 7
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zuciya: Dattijo mai shekaru 78 ya dawo gida bayan shekaru 26 da samun sabani da matarsa

"Maharan sun isa kasuwar ne a kan ababen hawansu kuma sai suka sauka tare da fara harbi ta ko ina. Bayan kashe-kashen da suka yi sai suka koma kan ababen hawansu suka kara gaba," ya ce.

Majiyar ta ce dogaro da rahoton da aka samu, maharan basu dauka ko tsinke ba a kasuwar.

Ya kara da cewa "A halin yanzu dai an samu gawawwakin mutane bakwai a wajen da abin ya faru kuma dagacin da kanshi ya zo ya ga kasuwar. Zan bada bayani dalla-dalla daga baya."

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da cewa zai kira don karin bayani daga baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel