An kuma: Matar aure ta cakawa mijinta wuka a yayin da yake bacci, bayan ta zarge shi da kwanciya da wata a titi

An kuma: Matar aure ta cakawa mijinta wuka a yayin da yake bacci, bayan ta zarge shi da kwanciya da wata a titi

- A birnin Owerri ne na jihar Imo aka samu wata mata da ta sokawa mijinta wuka har sau biyu a yayin da yake bacci

- Matar auren mai tsananin kishi ta zargi mijin nata ne da cin amanarta ta hanyar ajiye karuwa a waje

- kamar yadda wani ya wallafa a facebook tare da hotunan mijin, mijin ya tashi a dimauce ne yayin da yaji sukar don tseratar da rayuwar shi

Wani rahoto ya bayyana cewa wata mata mai tsananin kishi ta soki mijinta da wuka har sau biyu a yayin da yake bacci saboda zargin shi da take da ajiye karuwa a waje.

Kamar yadda mawallafin a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook mai suna Chinonso Chibuogwu ya wallafa, ya ce lamarin ya faru ne a Owerri jihar Imo. Mijin wanda aka sokawa wukar kuwa abokin shi ne.

Ya ce wanda abin ya faru da shi kuwa sunan shi jude Mmadu. Kuma matar shi din ta zarge shi ne da cin amanarta shiyasa ta soka mishi wuka har sau biyu a yayin da yake bacci.

Kamar yadda jaridar Gistamania ta ruwaito, bayan tashin shi ne firgice ya samu ya tsere tun kafin ta samu nasarar ci gaba da raunata shi.

KU KARANTA: Jami'ar tarayya ta jihar Nasarawa za ta bawa Sheikh Dahiru Bauchi takardar digiri ta karramawa

A yayin da ya wallafa hoton Jude a shafin shi na Facebook, Chinonso Chibuogwu ya wallafa: “Abin mamaki, na kaiwa abokina mai suna Jude Mmadu ne ziyara da safiyar nan a asibitin tarayya da ke Owerri. Matar shi ce tayi kokarin kashe shi saboda tana zargin shi da ajiye karuwa a waje. Mun godewa Ubangiji tunda bayan ta soke shi sau biyu yana bacci, ya tashi inda ya gudu don tsira da ran shi.”

Ya kara da cewa, “Jiya din nan nayi maganar. Mazan aure ku kiyaye saboda aljanun sukar maza da wuka na yawo. Ku dakata da cin amanar da kuke yi har sai mun shirya addu’a ta musamman a kan wannan sabon ci gaban.

“Na san cin amana ba shi kadai bane zunubi a duniyar nan kuma ba maza kadai bane ke cin amana. Masu cin amana da masu sukar abokan zamansu da wuka, ku gane.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel