Audu Isa Pele, Tsohon mataimakin kocin Plateau United ya rasu

Audu Isa Pele, Tsohon mataimakin kocin Plateau United ya rasu

- Audu Isa Pele, tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ya rasu

- Ya rasu ne a ranar Laraba 12 ga watan Fabrairu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya

- A halin yanzu kungiyar ta Plateau United ne ke mataki na biyu a teburin gasar NPFL

Kungiyar kwallon kafa ta Plateau United sun rasa mataimakin kocin su Audu Isa Pele da ta rasu a ranar Laraba 12 ga watan Fabrairun 2020 bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Labarin rasuwarsa ya jefa 'yan kwallon Najeriya cikin dimuwa da alhini duba da cewa yana da kuruciyarsa kafin ya rasu.

A cewar rahoton da Legit.ng ta gano, Audu Isa Pele, a cikin makon da ta gabata ya koka da cewa yana fama da ciwon kai inda ka garazaya da shi asibiti inda likitoci suka kwantar da shi a asibitin.

Sun bashi gado a asibitin bayan da gwaje-gwajen da suka gudanar a kansa ya nuna cewa yana fama da zazabin cizon sauro mai tsanani kuma akwai bukatar ya huta.

Bayan an masa magana a asibitin koyarwa ta Jos, an sallami Audu a ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu inda 'yan tawagarsa da iyalansa suka yi farin ciki.

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Da ya ke tsokaci a kan rasuwarsa, babban mai kula da harkokin kwallon kafa Sammy Adesoji wanda ke zaune a Jos ya tabbatar da cewa anyi jana'izar Audu Isa a Jos bisa koyarwan addinin musulunci.

Sammy Adesoji ya shaidawa Legit,ng cewa, "Abinda zan iya cewa a yanzu shine yanzu aka gama jana'izarsa kuma babban rashin ne a wurin mu a Plateau da sauran kuma Najeriya.

A halin yanzu, kungiyar ta Plateau United ce ke matsayi na biyu a gasar cin kofin NPFL inda ta ke da maki 33 bayan buga wasanni 19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel