PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari

Babban jam'iyyar hamayya ta People's Democratic Party (PDP) ta yi martani kan bidiyon da ya bazu inda aka nuna wasu mazauna Maiduguri suna yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ihun bayan da ya iso jihar domin yi musu ta'aziyya game da hare-haren da Boko Haram suka kai a jihar.

A cikin sanarwar da ta fitar, PDP ta ce ihun 'ba ma so' da aka yi wa Shugaba Buhari ya nuna karara cewa sun cire tsamani da gwamnatinsa.

Jam'iyyar ta kara da cewa abinda mazauna Maidugurin suka yi alama ce da ke nuna cewa 'yan kasar sun dora alhakin hare-haren da aka yi a shugaban kasar.

PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari
PDP ta yi martani kan ihun da 'yan Maiduguri suka yi wa Buhari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Wani sashi na sakon ya ce, "Jam'iyyar PDP ta na bukatar Buhari ya dauki matakai da suka dace domin kawo karshen kashe-kashen a jihar Borno da sauran sassan kasar bayan ziyarar da ya kai na jana'iza.

"Ihun da 'yan jihar Borno su kayi masa alama ce karara da ke nuna cewa sun dora alhakin samar da tsaro a kansu.

"Hakan ya kuma nuna cewa mutane sun cire tsamani a gwamnatin Buhari da jam'iyyar APC.

"Jam'iyyar ta APC ta bukaci shugaban kasar ya ziyarci wasu jihohin bayan Borno da suka da Kaduna, Kano, Benue, Plateau, Yobe, Adamawa, Zamfara, Kogi, Nigeri, Taraba da sauran jihohin da domin ya gane halin da 'yan Najeriya ke ciki kuma ya gane irin barnar da rashin daukan matakin kan tsaro ya haifar."

Jam'iyyar hamayyar ta ce idan Shugaban kasar ya yi wannan tafiyar ne kawai zai gane halin da kasar ke ciki kuma zai fahimci dalilin da yasa wasu ke neman ya yi wa hukumomin tsaron kasar nan garambawul.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel