Babu wanda ke tsangwaman Yari - Shugaban APC na bangaren Kabiru Marafa

Babu wanda ke tsangwaman Yari - Shugaban APC na bangaren Kabiru Marafa

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na bangaren da ke goyon bayan Sanata Kabiru Marafa ya yi Allah wadai da ikirarin da bangaren jam'iyyar dake biyayya ga Tsohon gwamna Abdul Aziz Yari, cewa gwamna Matawalle na tsangwamansu.

A ranar Talata, yan bangaren Yari sun kai ziyara ofishin shugaban uwar jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, a Abuja inda suka yi karar gwamnatin jihar kan tsangwamar da ake yiwa jigoginta.

Amma a jawabin da bangaren Marafa suka saki ta hannun shugabansu, Aljahi Surajo Maikatako, sun ce babu gaskiya cikin ikirarin bangaren Yari.

Sun ce kawai hasada Yari da yaransa sukeyi kan nasarorin da gwamnatin jihar mai ci take samu a bangaren tsaro.

Maikatako yace: "Bayan mun yi yarjejeniyar cewa a bari dukkan jam'iyyun siyasa suyi ayyukansu ba tare tsangwama ko barazana ba, wasu yan tsirarun yan siyasa na kokarin kafa gwamnatin wajen gwamnati kuma babu wani wanda yayi imani da demokradiyyar da zai goyi bayan hakan."

KU KARANTA: Ba tare da ziyartar Auno da aka kashe mutane ba, Buhari ya koma Abuja (Hotuna)

Yayinda yake kira ga Yari yaji tsoron Allah ya bari sabuwar gwamnati tayi aikin da ya gaza yi, ya ce wajibi ne a bari al'ummar jihar su samu zauna lafiya.

Shugaban bangaren Marafan ya yi kira ga kwamitin sulhun da jam'iyyar ta nada karkashin jagorancin Cif Bisi Akande yayi watsi da ikirarin Yari saboda komai na tafiya daidai kuma har yanzu akwai rabuwar kai tsakanin 'yayan jam'iyyar.

Hakazalika ya bayyanawa kwamitin sulhun cewa mafita daya ce da zata kawo sulhu jam'iyyar APC a jihar Zamfara ita ce gudanar da sabon zaben shugabannin jam'iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel