Gwamna Badaru ya nada sabon babban akantan gwamnatin jahar Jigawa

Gwamna Badaru ya nada sabon babban akantan gwamnatin jahar Jigawa

Gwamnan jahar, Jigawa, Abubakar Mohammed Badaru ya nada Aminu Sule a matsayin sabon babban akantan gwamnatin jahar, kuma nadin ya fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito gwamnan ya sanar da nadin ne ta bakin mai magana da yawunsa, Adamu Fanini cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Dutse, babban birnin jahar Jigawa a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta binciko fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a Arewa maso gabas

Kafin nadinsa wannan sabon mukami, Aminu Sule ne Darakta mai kula da asusu a ma’aikatar kudi ta jahar Jigawa.

A wani labarin kuma, Karamin ministan man fetir, Timipre Sylva ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gano fiye da gangan danyen mai biliyan daya a kwance a cikin yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Minista Sylva ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru daya gudana a karshen taron man fetir na kasa da kasa da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 12 ga watan Feburairu.

“Daga sakamakon da muke samu, duk da dai alkalumman basu gama fitowa ba, amma bincike ya nuna akwai fiye da gangan danyen mai biliyan 1 a kwance a yankin Arewa maso gabas, kuma mun fara fahimtar yadda yanayin kasar wurin take.” Inji shi.

Ministan yace har yanzu Najeriya ba ta kammala gano iya arzikin man ta ba, don haka yace akwai bukatar cigaba da gudanar da binciken neman danyen man fetir a sassan kasar nan domin gano sauran arzikin man.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel