Kashe-kashe: 'Yan Najeriya na cikin 'makoki' mara karewa - Shehu Sani

Kashe-kashe: 'Yan Najeriya na cikin 'makoki' mara karewa - Shehu Sani

- Tsohon dan majalisar dattijan Najeriya da ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu sani yayi magana a kan kashe-kashen da ake fama dashi

- Tsohon Sanatan ya ce 'yan Najeriya na rayuwa ne a tsorace tare da makokin da bashi da ranar karewa

- Tsohon dan majalisar ya jajanta kisan da 'yan bindiga suka yi a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna

Tsohon dan majalisar dattijai da ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar kasar nan karo ta takwas, Shehu Sani, ya jajanta yadda ‘yan Najeriya ke ta birne ‘yan uwansu.

Sani ya sanar da hakan ne ta shafinsa na tuwita a ranar Laraba yayin mayar da martani a kan harin da ‘yan ta’adda suka kai Kaduna. A wannan harin ne kuwa aka rasa rayukan jama’a a kalla goma tare da wasu kadarori.

Kashe-kashe: Najeriya na cikin 'makoki' mara karewa - Shehu Sani
Kashe-kashe: Najeriya na cikin 'makoki' mara karewa - Shehu Sani
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojoji sun sake ragargazan 'yan ta'adda, sun kamo wasu tare da makamai

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa mutane 16 ne suka rasa rayukansu bayan ‘yan ta’adda sun shiga kauyen Bakali da ke Fatika a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Sani ya jajanta halin da kasar nan ke ciki tare da cewa dole ne ‘yan Najeriya su kasance a tsorace.

Ya ce: “Rahoton cewa ‘yan ta’adda sun rufe tare da bankawa mutane 16 wuta da ransu a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna abin tashin hankali ne. Muna rayuwa ne a tsorace tare da zaman makoki a kullum.”

Ya kara da cewa, “A halin yanzu kasar nan na zaman makoki ne wanda bashi da ranar karewa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel