Yanzu-yanzu: Mutanen Borno sun yiwa Buhari ihun 'Bamayi' 'Bamaso' (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Mutanen Borno sun yiwa Buhari ihun 'Bamayi' 'Bamaso' (Bidiyo)

Karon farko a tarihi, an yiwa shugaba Muhammadu Buhari ihu a Arewacin Najeriya.

Faifan bidiyo dake yawo a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya nuna yadda mutanen jihar Borno suke yiwa shugaban kasan ihun 'Bamayi' 'Bamaso' a ranar Laraba, 12 ga watan Febrairu, 2020.

Kalli bidiyon:

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma babbar birnin tarayya Abuja bayan ziyarar jajen da ta'azziyar da ya kai jihar kan kisan akalla mutane 30 a garin Auno, hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Lahadi.

Buhari ya dira Borno ne daga kasar Habasha inda ya kwashe kwanaki biyar a taron kasashen nahiyar Afrika.

Buhari ya bar Borno misalin karfe 4 bayan la'asar ba tare ziyartar garin Auno, inda aka kashe mutanen ba ko gaishe da wadanda suka jikkata kuma suke kwance asibiti ba.

Misalin karfe 1 na rana gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin shugaban kasan tare da ministan walwala, Sadiya Umar Farouk da NSA, Babagana Munguno.

Daga nan ya garzaya fadar mai martaba Shehun Borno, Abubakar ElKanemi, sannan ya tafi gidan gwamnatin jihar domin jin abinci kafin ya fita daga jihar.

Shugaban kasan ya yi kira ga matasa su baiwa gwamnatinsa goyon baya saboda rana gobensu tayi kyau.

Yace: "Idan basu baiwa gwamnati goyon baya ba suna kokarin lalata rana gobensu ne. Shekaru na 77, shekaru nawa ya rage me in yi a duniyar yanzu?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel