Zuciya: Dattijo mai shekaru 78 ya dawo gida bayan shekaru 26 da samun sabani da matarsa

Zuciya: Dattijo mai shekaru 78 ya dawo gida bayan shekaru 26 da samun sabani da matarsa

A shekaru 26 da suka gabata, Edward Mwangi ya bar gidansa da ke kauyen Gikandu da ke Murang bayan ya samu sabani da matarsa. Ya fara tsayawa a Nairobi inda yayi aiki na shekaru uku kafin matar da yake wa aiki ta bashi wani aikin a gonarta da ke kauyen Gitangwanyi a Nakuru.

"Bamu shiri da matata na tsawon lokaci, a don haka ne na fita neman aiki kamar sauran maza," Mwangi ya ce.

A Gitangwanyi inda ya rayu kafin ya koma wajen iyalansa, abokansa sun matukar damuwa da yadda shekaru ke ja amma ya kasa komawa Murang inda iyalansa suke.

Waweru Kamau, daya daga cikin abokansa ne wanda ya kira sauran abokan har suka hada kudin da zai mayar da tsohon gida.

A ranar Alhamis da misalin karfe 6 na yamma, Mwangi ya isa garin Murang tare da Waweru kuma basu tsaya ko ina ba sai ofishin 'yan sanda.

Mutum daya da Mwangi ya iya tunawa shine tsohon abokinsa kuma makwabcinsa mai suna David Kirika wanda yake kasuwanci a Murang.

DUBA WANNAN: Miji da mata masu tabin hankali sun cika shekaru 22 suna zaune lafiya, sun haifi 'ya'ya 3

Sun bazama nemansa amma kuma sai basu yi sa'a ba don ya sauya gida. Basu hakura ba don har kauyen Gikandu suka je inda suka hadu da Kirika wanda ya nuna masa iyalinsa.

A kusan kowanne lokaci, yana dauke da karamin rediyo.

"Mwangi ya bar gida ne ba tare da wata magana ba kuma babu tsammanin zai dawo. Iyalansa sun dinga nemansa amma shiru. Ya dawo ya tarar da jikokinsa wadanda suka dinga neman kakansu na shekaru," Kirika ya ce.

Waweru ya ce duk da Mwangi kullum yana maganar gidansa da iyalansa a Murang, ya kasa tuna inda suke, jaridar Browngh ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel