Miji da mata masu tabin hankali sun cika shekaru 22 suna zaune lafiya, sun haifi 'ya'ya 3

Miji da mata masu tabin hankali sun cika shekaru 22 suna zaune lafiya, sun haifi 'ya'ya 3

Soyayya da zama a aure ba hankali kadai ake amfani da shi ba. Abin mamakin babba shine yadda wasu mahaukata biyu suka yi shekaru 22 da aure kuma har suka samu rabon 'ya'ya uku.

Samade da Cynthia dukkansu na da tabin hankali amma suna rayuwa ne a wani daki da suka gina da kansu a karkashin wata gada. Sun dau shekaru 22 a tare. Akwai lokuta da dama da 'yan kauyen suke ganinsu suna fada amma babu wanda zai ce ya ga lokacin da suke shiryawa.

Duk da cewa Samade da Cynthia ba 'yan kabila daya bane, amma haka suke rayuwa. An gano cewa kauyen da suke zama ne asalin garinsu Samade amma Cynthia kuwa 'yar yankin gabas din kasar nan ce. Sunyi rayuwar shekaru 22 ba tare da sun taba rabuwa ba.

Yadda suka sasanta kansu suke rayuwa tare ne har suka samu 'ya'ya uku babu wanda ya sani har yanzu. Ba su da sana'a tsayayya wacce suka dogara da ita sai dai roko. Hakazalika dukkansu babu mai hankali ko kankani.

Miji da mata masu tabin hankali sun cika shekaru 22 suna zaune lafiya, sun haifi 'ya'ya 3
Miji da mata masu tabin hankali sun cika shekaru 22 suna zaune lafiya, sun haifi 'ya'ya 3
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An gano motocin alfarma 100 na biliyoyin Naira da tsohon gwamna Yari ya karkatar

Ba a taba koya musu yadda zasu zauna da juna a matsayin ma'aurata ba amma kuma a hakan suke rayuwa har tsawon shekaru 22, kamar yadda jaridar Browngh ta ruwaito.

Samade da Cynthia dai sune Laila da Majnun a duniyarsu, sun kuma dace sosai da juna. Basu da hankali amma kuma suna alfahari da juna da kuma aurensu.

Ba sau daya ko biyu ba, ana ganinsu suna sumbatar juna, runguma da kuma nuna wa juna asalin soyayya a kauyen.

Komai nasu a hade yake, suna wanka tare, wasa, cin abinci, tarbar bakinsu, fada, dariya da kuma sauransu duk a tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel