Dalilin da yasa muka cire Ahmad Lawan matsayin shugaban kwamitin sulhu - Oshiomole

Dalilin da yasa muka cire Ahmad Lawan matsayin shugaban kwamitin sulhu - Oshiomole

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta bayyana dalilin da yasa aka cire shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, daga matsayin shugaban kwamitin sulhun jam'iyyar.

Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya ce an maye Ahmad Lawan da Cif Bisi Akande ne saboda ayyuka sun masa yawa.

Za ku tuna cewa a ranar 18 ga Disamba, 2019, APC ta nada kwamitin mutane 10 karkashin jagorancin Ahmad Lawan domin sulhu tsakanin 'yayn jam'iyyar a jihohi 36 da birnin tarayya.

Amma gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya nuna rashin amincewarsa da mambobin kwamitin saboda akwai wasu yan adawarsa a ciki musamman dangane da rikicin APC a jiharsa.

Rikici ya barke a cikin gidan APC a jihar Edo tsakanin shugaban uwar jam'iyyar da Gwamnan jihar, Obaseki.

Oshiomole ya yi watsi da rahoton cewa an canza kwamitin ne saboda kin amincewar gwamnan inda yace dalilin kawai shine kwamitin ta yi jinkiri da yawa wajen aiwatar da aikinta.

Yace: "Kwamitin ta samu koma baya ne saboda wanda aka zaba ya jagoranci kwamitin ya gaza yi saboda ayyukan kasa."

Ya mika godiyarsa ga dukkan mambobin sabon kwamitin da suka amince da nadasu cikin kwamitin.

Dalilin da yasa muka cire Ahmad Lawan matsayin shugaban kwamitin sulhu - Oshiomole
Ahmad Lawan matsayin shugaban kwamitin sulhu - Oshiomole
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun bankawa mutane 16 yan gida daya wuta har lahira a Kaduna

A bangare guda, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sojoji, Sanata Ali Ndume, ya jadadda bukatar a gudanar da bincike kan harin da yan ta’adda suka kai Auno wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 30.

Ya ce bala'in da rikicin Boko Haram ya jefa jama’ar yankin arewa maso gabas musamman ma jahar Borno, ya isa haka nan inda ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin kawo karshensa.

Harin da yan ta’addan suka kai Auno na daya daga cikin hare-hare mafi muni da aka kai a baya-baya nan.

Mayakan sun kai harin ne da yayin da matafiyan ke barci cikin motocinsu bayan jami'an tsaro sun hana shiga birnin Maiduguri daga misalin karfe biyar na yammaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel