Da duminsa: Yan bindiga sun bankawa mutane 16 yan gida daya wuta har lahira a Kaduna

Da duminsa: Yan bindiga sun bankawa mutane 16 yan gida daya wuta har lahira a Kaduna

Kimanin mutane 16 yan gida daya sun rigamu gidan gaskiya bayan yan bindiga sun bankawa musu wuta yayinda suka kai hari kauyen Bakali, dake Fatika, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

An samu labarin cewa yan bindigan sun dira kauyen ne ranar Talata misalin karfe 4 na yamma kuma suka fara banka wuta kan kayayyakin masarufi, motoci, da babura.

Yan bindigan sun kulle yan gida daya a cikin daki kafin banka musu wuta. Daily Trust ta ruwaito.

Wani dan garin, Alhaji Sani Bakali, wanda ya bayyana cewa yan bindiga kimanin 100 suka kai farmaki garin kuma sunyi barna.

Har yanzu hukumar yan sanda ba tayi tsokaci kan lamarin ba.

A bangare guda, Akalla matafiya guda 10 ne wasu gungun miyagu yan bindiga suka yi awon gaba dasu a kan babbar hanyar Obajana zuwa Abuja dake cikin garin Obajana na jahar Kogi, inji rahoton Punch.

Majiyarmu ta ruwaito har zuwa lokacin tattara rahoton babu wata masaniya game da sunayen fasinjojin motar, amma dan kasuwan dake da motar, Abdulganiyu Hakeem ya bayyana cewa motar ta tashi ne daga Ajowo Akoko.

KU KARANTA: Coronavirus: An gwada mutane uku - Ministan Lafiya, Osagie Enahire ya bayyana a Kano

Hakeem ya bayyana cewa: “Fasinjojin motar su 10 tare da direban duk suna hannun masu garkuwan a cikin kungurmin daji, daga cikin fasinjojin akwai wani dalibin kwalejin horas da lauyoyi dake Abuja.

“Mun samu labarin yan bindigan sun tattara kusan fasinjoji 30 daga motoci da dama da suka tare a kan hanyar, a cikin makon daya gabata.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel