Yanzu-yanzu: Kotu ta yankawa FG diyya ta biya Sowore

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankawa FG diyya ta biya Sowore

Mai Shari'a Ojukwu ta babban kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya Omoyele Sowore da Olawale Bakare dubu dari bibbiyu, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Dukkansu biyun dai suna gurfane ne a gaban kotun sakamakon zarginsu da ake da cin amanar kasa, batanci ga shugaban kasa da sauransu.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa sananne kuma mashahurin marubuci, Wole Soyinka da kuma Sanata Shehu Sani sun isa babbar kotun tarayya da ke Abuja don kallon shari'ar Omoyele Sowore, makirkirin juyin juya-hali.

Soyinka ya isa kotun ne da karfe 8:50 na safiyar yau Laraba kafin isowar Sowore kotun.

Yanzu-yanzu: Kotu ta yankawa FG diyya ta biya Sowore
Yanzu-yanzu: Kotu ta yankawa FG diyya ta biya Sowore
Asali: Original

DUBA WANNAN: Shehu Sani da Wole Soyinka sun isa kotu don kara ga Sowore (Hotuna)

Sowore da Olawale Bakare ana zarginsu ne a kan laifuka bakwai da suka hada da damfara, batanci ga shugaban kasa da sauransu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya ce ta cafke shi a ranar 3 ga watan Augusta sakamakon zanga-zangar da suka shirya a fadin kasar nan.

An sake shi ne bayan da yayi kwanaki 124 a wajen hukumar. Sun kuwa kara cafke shi kasa da sa'o'i 24 bayan sakin shi a babbar kotun tarayya da ke Abuja. Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel