Ramuwar Gayya: Budurwa ta kira babbar kawarta a waya a lokacin da take lalata da mahaifinta, bayan kawar ta kwace mata saurayi

Ramuwar Gayya: Budurwa ta kira babbar kawarta a waya a lokacin da take lalata da mahaifinta, bayan kawar ta kwace mata saurayi

- Cin amana dai tun farkonta ba halin kirki bane kuma ba ta da dadi, amma idan ya faru akwai kyau mutum ya yafe

- Wata budurwa ta wallafa wani bidiyo mai tsawon sakanni 17 tana tare da mahaifin kawarta a dakin otal

- Kamar yadda ta ce, kawarta ta ci amanarta ne ta hanyar kwanciya da saurayinta, amma ita ta rama da mahaifinta ne

Wata budurwa wacce bata bayyana sunanta ba tayi kira ga kawarta wacce ta kira da Ada da ma ci amana. Ada dai ta kwanta da saurayin kawar ta ne, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

A cikin bidiyon da ta wallafa, kawar ta nuna mahaifin Ada din da kuma bayyana yadda take kwanciya da shi a matsayin hanyar mayar da martani da ramuwar gayya ga kawar. Ta ce ta yi hakan ne saboda ta zargi kawar da cin amanarta ta hanyar kwanciya da saurayinta.

A bidiyon mai tsawon sakanni 17, an ji budurwar na cewa “Ada kin kwanta da saurayina. Amma ni a halin yanzu ina tare da mahaifinki ne a dakin otal. Masoyina kayi mata magana.”

A wannan lokacin kuwa sai wanda ake zargin da zama mahaifin kawarta din ya ce ‘Barka dai’ a bidiyon.

Ba wannan ne karo na farko ba dai da aka taba ji ko ganin kawayen juna na yin ramuwar gayya a kan cin amana.

A wani labari na daban da Legit.ng ta ruwaito, an ji cewa bankin FCMB ya dau nauyin wata karamar yarinya da aka ga hotonta tana aikin makarantarta a gaban hasken ATM.

Dele karamar yarinya ce ‘yar makaranta wacce aka ga tana amfani da hasken ATM din bankin FCMB wajen yin aikinta na makaranta. Mazauniyar jihar Ondo ce da kakarta, kuma hotunanta sun jawo cece-kuce a kafofin sada zumuntar zamani.

A yayin da karamar yarinyar ke amfani da hasken ATM din, wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ya ganta tare da daukar hotonta. Ya wallafa hoton wanda ya yadu a kafar sada zumuntar.

Bayan wannan hoton ya kai ga hukumar bankin ne, sai suka nemi a nemo musu inda zasu ga Dele yadda zasu dau nauyin karatunta, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta wallafa.

Kamar yadda ya wallafa: “Na ga karamar yarinyar nan mai suna Dele a kan titin Yaba da ke birnin Ondo. Tana amfani da hasken ATM ne don yin aikin da aka ba ta a makaranta. Na mutunta jajircewarta da nacinta.”

Sai hukumar bankin suka mayar da martani ta shafinsu na tuwita kamar haka: “A gaskiya mun lura tana da son karatu. Muna farin ciki ta yadda ATM dinmu ya zama haske gareta, amma zamu so taimakonta. Za ka iya nemo mana Dele? A yi ta wallafawa har ya kai ga inda aka santa.”

Rahotanni da yawa sun tabbatar da cewa Dele na zama ne tare da kakarta kuma an gano su. A halin yanzu tana zuwa wata makaranta ne mai suna Hope of Glory Academy a Ondo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel