Cacakar Buhari: Majalisar Koli ta musulunci ta yi wa Bishop Kukah martani

Cacakar Buhari: Majalisar Koli ta musulunci ta yi wa Bishop Kukah martani

Majalisar koli ta harkar musulunci a Najeriya, NSCIA, a daren ranar Talata ta ce kalaman da Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan Kukah ya yi game da Buhari ba gaskya bane.

Shugaban sashin sadarwar na NSCIA, Ibrahim Aselemi ne ya bayyana hakan a cikin sakon martanin da ya aike wa The Punch misalin karfe 11 na daren ranar Talata.

A jawabin da ya yi a ranar Talata din, Kukah ya cacaki Buhari yayin wa'azin da ya yi a Shephard Major Seminary, Kaukau a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna wurin jana'izar Micheal Nnadi, wani dalibin makarantar horar da malaman addinin kirista na darikar katolika da masu garkuwa da mutane suka kashe.

Cacakar Buhari: Majalisar Koli ta musulunci ta yi wa Bishop Kukah martani
Cacakar Buhari: Majalisar Koli ta musulunci ta yi wa Bishop Kukah martani
Asali: Twitter

Ya tunatar da mutane alkawurran da Buhari ya yi yayin yakin neman zabe a 2015. Ya ce lokacin yakin neman zaben Buhari ya ce muddin aka zabe shi, Duniya ba za ta damu da batun rashin tsaro a Najeriya ba.

DUBA WANNAN: A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Kukah ya ce bayan shekaru biyar, shugaban kasar ya rika nuna fifiko wurin nadin jami'an sojoji da hukumomin tsaro.

A martanin da Aselemi ya aike wa majiyar Legit.ng ya ce ya kamata shugabanin addini su rika furta kalamai da su hada kan mutane.

Ya ce, "Ya ce kalamen Rev. Fr. Mathew Hassan Kukah abin takaici ne a matsayinsa na shugaba da muke girmamawa. A matsayin mu na shugabannin addini, kamata ya yi kalaman mu su kunshi abubuwa uku, hadin kai, tsaro da kaunar kasar mu.

"Ya tsara kalamansa ne da nufin karya gwiwar 'yan Najeriya game da gwamnatin Buhari. Shin Emefiele da Obiora musulmai ne daga Arewa? Buhari ya nada su matsayin shugaban babban bankin Najeriya da mataimaki. Rev. Fr Kukah baya son fadin gaskiya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel