A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

A karo na farko, Sadiya Farouq ta yi magana kan jita-jitar auren ta da Shugaba Buhari (Bidiyo)

Ministan ma'aikatar ayyukan agaji da kula da bala'i, Sadiya Farouq, ta yi tsokaci a kan jitar-jitar cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai aure ta.

Labarin na bogi ya karade dandalin sada zumunta a shekarar 2019, inda wasu ke ta ikirarin cewa Shugaban kasar ya gaji da wasu halaye da Aisha hakan yasa ya yanke shawarar kara mata ta biyu.

An saka ranar auren na karya tare da yada takardan gayyatan aure na karya a dandalin sada zumunta a lokacin.

Daga karshe dai Minista Sadiya Farouq ta yi tsokaci a kan batun a wani tattaunawa da ta yi da Daily Trust inda ta ce batun auren labarin kanzon kurege ne mara tushe balle makama duk da cewa ita kam mutum ne na gaskiya.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sojoji sun kama mayakin Boko Haram a Filato

Ta kara da cewa gugguwan labarin ya zo ya kuma wuce amma ita tana nan daram dam.

Da aka yi mata tambaya kan ko ta hadu Aisha Buhari tun bayan da jita-jitar ya karade gari, Sadiya ta bayar da amsa da cewa "A'a".

Ta ce ba ta samu damar haduwa da First Lady din ba duba da cewa tana da ayyuka sosai a gabata kazalika ita ma matar shugaban kasar tana da nata ayyukan da suka dabaibaiye ta.

Ga dai faifan bidiyon hirar da aka yi da ita a kasa kamar yadda muka samu daga Lailasnews.com

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel