CBN za ta dena kona lalatattun takardun naira, za ta fara amfani da fasahar canja datti
Babban Bankin Najeriya (CBN) ta ce za ta dena kone tsaffin kudaden takardun naira a maimakon hakan za ta fara canja su domin buga wasu sabbin kudaden.
A wani sako da ta fitar a shafin ta na intanet, babban bankin ta yi kira ga kamfanoni da suka kware a fasahar canja datti su gabatar da takardun kwangilar su domin samun aikin canja tsaffin kudaden na takarda.
Wannan fasahar da canja datti (recycling) ana amfani da ita a bangarori dabandaban da suka hada da canja robobi, karafa, littafai da sauransu.

Asali: Twitter
"Sashi na 18(d) na dokar CBN ta 2007 ya bawa babban bankin damar lalata takardun naira ko kwandala da suka lalace a karkashin sashi na 20(3), " kamar yadda sakon da bankin ta fitar ya ce.
"CBN na tattara daruruwan ton na lalatattun kudaden naira a duk mako a wuraren zubar da sharar ta 12 da ke kasar.
DUBA WANNAN: Bidiyon mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna tana kashe gobara ya jawo cece-kuce
"An kone lalata takardun nairan ne ta hanyar kone su a fili a wurarren da bankin ta tanada ko kuma wuraren da ta karba haya daga gwamnatin jihar."
A cikin sakon da babban bankin ta fitar, ta ce kone takardun nairorin a fili ya na gurbata muhalli.
Ta ce an gano cewa canja datti ya fi alfano ga tattalin arziki da kuma muhalli.
Ta yi bayanin cewa ta wannan sabon fasahar, "Za a sauya takardun nairan zuwa wasu ababe masu amfani."
Bankin za ta rufe karbar takardun neman kwangilar a ranar 11 ga watan Maris na 22.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng