Yan ta'adda sun fara amfani da Soshiyal Midiya wajen daukan mambobi - Pantami

Yan ta'adda sun fara amfani da Soshiyal Midiya wajen daukan mambobi - Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, ya ce kungiyoyin yan ta'adda na amfani da kafofin ra'ayi da sada zumunta wajen daukan sabbin mambobi domin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Pantami ya bayyana hakan ranar Talata yayinda yake gabatar da muhadara kan yaki da ta'addanci a cibiyar NARC Abuja.

Ministan yace: "Ya bayyana karara cewa yan ta'adda na amfani da soshiyar midiya wajen daukan sabbin ma'aikata domin kai hare-hare."

"Wannan sabon abu na bukatar hanyoyin zamani wajen kawar da ta'addancin."

"Hukumar Soji da hukumomin leken asiri za su iya amfani da yanar gizo wajen yakar ta'addanci. Za'a iya amfani da yanar gizo wajen sanin shirye-shirye da yadda wadannan kungiyoyi ke gudanar da ayyukansu."

KU KARANTA: Forbes ta saki jerin masu kudin nahiyar Afrika, akwai yan Najeriya 4, 2 Kanawa ne (Kalli Jerin)

Mun kawo muku rahoton cewa Ministan sadarwa, Dakta Isa ali Pantami, ya umurci hukumar sadarwan Najeriya NCC ta tabbatar da cewa kada kowani dan Najeriya ya mallaki fiye da layukan waya 3.

Ministan ya bada umurnin ne a ranar Laraba a jawabin da hadimin, Dakta Femi Adeluyi, ya rattaba hannu inda ya umurci NCC ta sake duba dokar rijistan layukan waya.

Jawabin ya kara da cewa akwai bukatan hakan ne bisa ga rahoton da aka samu daga hukumomin tsaro, bayan samun nasarar kawar layukan da ba'ayi rijista ba a Satumban 2019.

Ministan ya kara cewa hukumar NCC ta tabbatar da cewa sai mutum ya mallaki lamban zama dan kasa NIN kafin ya iya rijistan layi. Wadanda kuma ba yan kasa ba, a yi amfani da bizansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel