Boko Haram: A 2019, yara 1,115 suka mutu saboda tsananin yunwa a Borno - UNICEF

Boko Haram: A 2019, yara 1,115 suka mutu saboda tsananin yunwa a Borno - UNICEF

Kwamitin tallafin yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, a ranar Talata ya bayyana cewa yara 1,115 ne suka mutu sakamakon yunwa tsakanin watan Junairu da Disamban 2019.

Shugaban sashen lafiyar abinci na UNICEF, Simon Karanja, ya bayyana hakan ne a taron rantsar da kwamitin abinci da yakin yunwa na jihar Borno a Maiduguri.

Simon Karanja ya ce a shekarar 2019, an yi jinyan yara 138,236 a shirye-shiryen yaki da yunwa a cibiyoyi daban-daban a jihar yayinda 6,399 suka ki zuwa jinya.

Ya ce a kowace rana, sai yara akalla uku sun mutu a jihar Borno.

Babban jami'in ya laburta cewa dalilin da ya sa aka samu tabarbarewan lafiyar abinci shine rashin cin abinci mai kyau, cututtuka irinsu gudawa, bakon dauro da rashin abinci.

Wasu dalilan sun hada da rashin kula da rashin magunguna da yara masu fama da rashin lafiya.

Yace: "A 2020, ana shirin kula da yara 533,000 dake bukatar kulawa."

"Hakazalika ana kyautata zaton jinyar yara 138,000 masu fama da ciwon yunwa mai tsanani yayinda 182 za suyi jinyar ciwon maras tsanani."

Boko Haram: A 2019, yara 1,115 suka mutu saboda tsananin yunwa a Borno - UNICEF
Boko Haram: A 2019, yara 1,115 suka mutu saboda tsananin yunwa a Borno - UNICEF
Asali: Depositphotos

Mun kawo muku rahoton cewa Tsohon gwamnan jahar Borno, kuma wakilin mazabar Bornon ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kashim Shettima ya yi kira ga shelkwatar tsaro ta Najeriya da ta gudanar da cikakken bincike game da harin Auno, domin kuwa akwai tambayoyi dake bukatar amsoshi game a harin.

Shettima ya bayyana haka ne cikin wata gajerar sanarwa daya wallafa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook da yammacin Talata, 11 ga watan Feburairu, inda yace tabbas an samu karuwar hare haren Boko Haram a yan kwanakin nan a wasu sassan jahar Borno.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana bacin ransa bisa yadda Sojoji suke aiki a jahar Borno, har ma ya daka ma babban kwamandan yaki da Boko Haram tsawa saboda yadda suke cutar da jama’a a jahar.

Gwamnan ya nuna bacin ransa ne a ranar Litinin, 10 ga watan Feburairu yayin ziyarar gani da ido da ya kai garin Auno na jahar Borno inda mayakan Boko Haram suka kai farmaki suka kashe mutane fiye da 30.

A yayin ziyarar, Zulum ya zargi Sojoji da barin mutane a hannun Boko Haram, inda yace Sojojin daya kamata su samar da tsaro a Auno, amma sai ka ga sun yi tafiyarsu da an ce karfe 5 na yamma ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel