Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a filin jiragen sama na Owerri

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a filin jiragen sama na Owerri

- Gobara ta tashi a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Sam Mbakwe Intarnational Cargo da ke Owerri

- Babbar manajar hukumar ta ce gobarar ta fara ne sakamakon wutar daji da ta shafi filin jirgin

- Hukumar tayi kira ga ma'aikatan da su kiyayi kunna wutar daji a farfajiyar jirgin saboda hakan na kawo kalubale

Mummunar gobara ta barke a wani sassa na filin sauka da tashin jiragen sama na Sam Mbakwe Intarnational Cargo da ke Owerri a jihar Imo, kamar yadda Sahara Reporters suka ruwaito.

Babbar manajar hukumar filayen sauka da tashin jiragen sama ta Najeriya, Henrietta Yakubu, ta ce gobarar ta barke ne sakamakon wutar daji da ta shafi filin jirgi.

Yakubu ta ce a halin yanzu masu kashe gobara na kokarin ganin sun kasheta.

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a filin jiragen sama na Owerri
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a filin jiragen sama na Owerri
Asali: UGC

Ta ce, “Jami’an hukumar kwana-kwana na ta kokarin ganin sun kashe wutar a halin yanzu. Amma kuma wannan al’amarin ba zai shafi tashi da saukar jiragen ba na yau din.”

DUBA WANNAN: Daga karshe: Jonathan ya bayyana dalilin sauke Farida Waziri

Hukumar filayen jiragen saman Najeriya na kira ga ma’aikatan filayen jiragen da su guji saka wuta a dattin da aka tattara a farfajiya ko kewayen filayen don hakan na kawo manyan kalubale.

A wani labari na daban, kun ji yadda wata budurwa ta saka katon hijabi tare da shiga cikin jigin sama da Shisha.

Bayan jirgin ya daga ne ta shiga makewayi inda ta fara zuka. Mintoci kadan da farawarta ne masu kula da jama'a na cikin jirgin suka ganta inda suka hanata abinda take yi.

Babu jimawa kuwa jirgin ya fara hayaki, lamarin da yayi sanadin juyawarsa zuwa filin da ya tashi don saukar gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel