FG na sake masu kashe mu - Sojoji sun nuna bacin ransu kan sakin yan Boko Haram 1400

FG na sake masu kashe mu - Sojoji sun nuna bacin ransu kan sakin yan Boko Haram 1400

Wasu dakarun Sojojin Najeriya dake faggen faman yaki a yankin Arewa maso gabas sun nuna bacin rai da rashin jin dadinsu kan sakin tubabbun yan Boko Haram 1,400 da gwamnatin tarayya tayi.

Kwamishanan yada labaran jihar Borno, Babakura Jato, ya bayyanawa manema labarai ranar Litinin cewa an saki tubabbun yan Boko Haram 1,400 tun lokacin da aka kaddamar da shirin sauya tunanin yan ta'addan da aka kama mai taken 'Operation Safe Corridor'

An tsara shirin 'Operation Safe Corridor' ne domin sauya tunani da ilmantar da tsaffin yan Boko Haram.

Tsokaci kan lamarin, Sojojin dake faggen fama sun tabbatar da labarin kuma sun ce basu san dalilin da zai sa a rika sakin yan Boko Haram da yawa haka ba.

FG na sake masu kashe mu - Sojoji sun nuna bacin ransu kan sakin yan Boko Haram 1400
FG na sake masu kashe mu - Sojoji sun nuna bacin ransu kan sakin yan Boko Haram 1400
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Bam ya tashi a jihar Edo

Daya daga cikin Sojin yace:"Sojoji da yawa basu ji dadin abinda ke faruwa ba. Muna barikin Maimalari yayinda aka saki wasu yan Boko Haram."

"Jami'an gwamnati na sakinsu, amma yan Boko Haram na kashe Sojojin da suka kama. Wannan abu ya sabawa hankali."

"Yayinda muke shiga daji domin kawar da wadannan mutanen, gwamnati na sakinsu. Shin aikin banza muke kenan?"

Wani Sojan yace ya yi imanin cewa wadanda aka saki zasu koma gidan jiya.

"Za kayi mamakin ta yaya yan Boko Haram ke kara yawwa kulli yaumin? Idan muka damkesu kuma kawosu nan, wasu manya zasu fara tattaunawa kan yadda za'a sakesu.

Ina tabbatar maka da cewa wasu daga cikin wadannan mutanen komawa daji sukeyi, babu tuban da sukayi."

Mun kawo muku rahoton cewa Bayan jawabin mai martaba sarkin Kano, Bankin duniya ta saki rahoton cewa kimanin kashi 87 masu fama da talauci a Najeriya yan Arewacin kasar ne.

A rahoton da bankin ta saki, ta bayyana cewa yankin kudu maso kudu ce yankin da ta samu raguwan talauci tsakanin shekarar 2011 da 2016.

Yace: "Talauci a Arewacin Najeriya na karuwa musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar."

"Kimanin rabin masu fama da talauci na Arewa maso yamma kuma kashi 87 na talakawan kasar na Arewacin Najeriya."

"Talauci a kudancin Najeriya kimanin kashi 12 ne. Yankin kudu maso kudu ce yanki mai karancin talauci tsakanin 2011 da 2016."

"Kashi 64 na dukkan talakawan Najeriya na zaune a karkara kuma kashi 52 na masu zama a karkara talakawa ne."

Asali: Legit.ng

Online view pixel