An gano bidiyon shugaban dalibai na jami'a a cikin 'yan kungiyar asiri

An gano bidiyon shugaban dalibai na jami'a a cikin 'yan kungiyar asiri

- Sabon zababben shugaban kungiyar daliban babbar makarantar gwamnatin tarayya da ke Ilaro ya shiga hannun ‘yan sanda

- An kama shugaban kungiyar daliban ne bayan sun hallara taron wata kungiyar asiri da yammacin ranar Lahadi

- An zabe shi ne a watan Disamban da ta gabata amma sai dubun shi ta cika inda ya shiga hannun jami’an tsaro

Sabon zababben shugaban kungiyar daliban babbar makarantar gwamnatin tarayya da ke Ilaro, an kama shi dumu-dumu a yayin taron wasu ‘yan kungiyar asiri da ke jihar Imo.

Wata majiya ta sanar da jaridar Within Nigeria cewa shugaban kungiyar daliban mai suna Adegboye Emmanuel Olatunji da sauran ‘yan kungiyar asirin ta Black Axe, sun shiga hannun jami’an tsaro ne a yammacin ranar Lahadi.

An zabi Olatunji ne a watan Disamba na 2019 don fara mulkin kungiyar daliban makarantar.

Daga bidiyon da aka dauka, an ga shugaban kungiyar daliban da sauran ‘yan kungiyar a hannun ‘yan sanda kuma an tura su cikin mota.

An ga masu kallo a inda ‘yan sandan suka kama shugaban kungiyar daliban tare da sauran ‘yan kungiyar asirin.

KU KARANTA: Tirkashi: An kama 'yan Chinese guda biyu da suka yi luwadi da wani dan Najeriya ta hanyar yi masa fyade

Amma kuma duk kokarin da aka yi don jin ta bakin rundunar ‘yan sandan, hakan ya ci tura.

A wani labari na daban, wasu ‘yan kungiyar asiri da suka shiga hannun jami’an tsaro sun bayyana yadda suke daukar ‘yan makarantar sakandire don shiga kungiyarsu

Kamar yadda shugaban kungiyar asirin ya sanar da ‘yan sandan, suna mafani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ne don samun mambobi.

Ya ce shi dai ya shiga kungiyar tun yana da shekaru 12 kuma yana aji biyu na sakandire. A lokacin kuwa da yake amsa laifin shi, yana da shekaru 24 kuma ya zama shugaban kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel