An kashe matashi dan kwallon kafa a gaban iyayenshi, lokacin da ake jana'izar kakanshi

An kashe matashi dan kwallon kafa a gaban iyayenshi, lokacin da ake jana'izar kakanshi

- An harbe wani matashin dalibi kuma dan kwallon kafa mai tasowa a wajen birne kakanshi

- Matashin mai shekaru 15, da zai je raka wasu ‘yan uwanshi ne wata kwaleji amma sai ya fasa don zuwa birne kakanshi

- Faston cocin ya ce yayi tsammanin za a yi rigima a wajen, shiyasa ya kawo jami’an tsaro amma suna tafiya abun ya faru

An harbe wani matashi a yayin bikin birne kakan shi. An gano cewa matashin yaron dan kwallon kafa ne mai tasowa kuma yana makarantar sakandire ne.

Terrance Jackson mai shekaru 15 ya mutu ne a ranar Asabar bayan da aka harbe shi. Wannan harbin kuwa shi ya hargitsa wajen makokin kakan shi da aka yi a Riviera Beach, in ji wata ‘yar sanda mai suna AJ Walker a ranar Litinin.

Royce Freeman mai shekaru 47 shima ya mutu a take. Wata mata kuwa ta samu rauni mai tarin yawa wanda ake gani a matsayin barazana ga rayuwarta.

Har yanzu dai ba a kama ko mutum daya ba amma Walker ta ce masu bincike na aikinsu.

Tronica da Terrance Jackson Sr. sun sanar da CBS Miami cewa su ganau ne ba jiyau ba a yadda mutuwar dansu ta zo.

KU KARANTA: Bankin FCMB ya dauki nauyin karatun dalibar da take rubuta jarrabawa a gaban bankin da daddare

“A lokacin da na isa wajenshi, nayi kokarin cire mishi botirin wuyan rigar shi, ina kuma ce mishi yayi numfashi. Ya girgiza kanshi amma a haka ya ciki.” Cewar Tronica.

Terrance Jackson Sr. ya ce: “A lokacin kawai dukkan rayuwar shi ce ta dawo min. Na tuna lokacin da aka haifeshi a gabaan ya fara numfashi amma sai gashi a gabana numfashin shi ya dauke.”

Jackson wanda aka fi kira da Teejay, ya kamata a ce ya raka wasu ‘yan uwan shi 20 ne zuwa wata tafiya amma sai ya tsaya don birne kakanshi.

An fara harbin ne da rana a tsallaken titin cocin Victory, inda ake birne kakan nashi. Faston cocin mai suna Tywuante D. Lupoe ya sanar a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.

Ya kara da cewa sun san akwai yuwuwar a yi tashin hankali don haka ne suka kawo jami’an tsaro. Jami’an tsaron sun tafi kenan aka fara harbin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel